Wata mata mai suna Zainab Ibrahim ta rasa ranta a kokarin raba fada tsakanin ‘ya’yanta maza biyu, Inusa da Usman.
Duk da cewa babu cikakken bayani kan abin da ya hada su, bayanai na nuna cewa Inusa ya soka wa mahaifiyarsa wuka a hannunta na dama bisa kuskure.
- Wasan Dambe: Dogon Dan Ladi Ya Doke Autan Kudawa
- Shugaban EFCC Ya Nemi Cin Hancin $2m A Wajena, Ina Da Hujja –Matawalle
Lamarin ya faru ne a yankin Kpaduma da ke unguwar Asokoro a Abuja.
Wani mazaunin unguwar Saliu Shehu ya ce an gaggauta kai Zainab asibiti amma daga baya sai rai ya yi halinsa.
A lokacin da aka tuntube ta, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda Abuja, Josephine Adeh, ta ce Inusa ya tsere amma ana bincike kan lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp