Uwargidar Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Fatima Dikko Radda, ta buƙaci a yi haɗin gwiwa don yaƙi da cutar nono da ta mahaifa, cututtuka da ke kashe mata da dama a Nijeriya.
Ta yi wannan kiran ne a wani taro da aka shirya a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, wanda Sashen Kula da Mata ya shirya, domin wayar da kan mata.
- Bello Turji Bai Yi Sulhu Da Kowa Ba – Guyawa Isa
- Matar Marigayi MKO Abiola, Ta Rasu Tana Da Shekaru 82
Taron dai ya gudana a ɗakin taro na Kwalejin Postgraduate College, karkashin taken: “Mata da Wayar da Kai Kan Ciwon Nono da Karfafa Mata.”
Hajiya Fatima ta ce tana alfahari da kasancewarta tsohuwar ɗalibar jami’ar, kuma ta nuna farin cikinta da samun damar jagorantar wannan taro.
Ta ƙara da cewa wannan taron ba don tattaunawa kawai aka shirya shi ba, illa don ɗaukar mataki game da ciwon nono da na mahaifa, waɗanda ke barazana ga rayuwar mata.
A jawabin da Shugaban Jami’ar ABU, Farfesa Adamu Ahmed, ya yi ta bakin mataimakinsa, Farfesa Sanusi Rafindadi, ya yaba da yadda taron ke taimakawa wajen wayar da kai game da wannan cuta mai hatsari.
Ya kuma gode wa Hajiya Fatima bisa amsa gayyatar jagorantar taron.
Shugabar Sashen Kula da Mata, Farfesa Rahanatu Lawal, ta jaddada buƙatar haɗin kan kowa da kowa wajen yaƙi da cutar.
Ta ce mata ba za su iya wannan yaƙi su kaɗai ba, dole ne maza su ba su goyon baya.
Daga cikin waɗanda suka gabatar da jawabi akwai Dakta Aminat Jimoh daga Asibitin Koyarwa na ABU.
Ta buƙaci mata da su riƙa duba kansu akai-akai, musamman idan suna da tarihin ciwon a cikin danginsu.
Ta kuma roƙi Hajiya Fatima ta taimaka wajen sauƙaƙa wahalar samun magani da mata ke fuskanta.
Wata ‘yar kasuwa, Hajiya Rabi Kabiru, ta buƙaci mata da su riƙa dogaro da kansu ta hanyar sana’o’i domin hakan zai taimaka musu wajen kula da lafiyar kansu da ta iyalansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp