• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Waƙa Sana’a Ce Sai Da Ilimi Da Jari -Wizzamany

by Rabilu Sanusi Bena
1 year ago
Waka

Matashin mawakin dan asali Jihar Taraba Sham’un Muhammed da aka fi sani da Wizzamany, ya ja hankalin matsa da suke da sha’awar tsunduma harkar waka domin aika sako, da su nemi ilimi sannan su nemi kudi, domin a cewarsa waka sana’a ce idan ba ka da jari sai dai ka ji ana yi.

Wizzamany, ya bayyana haka a tattaunawarsu da wakilinmu RABIU ALI INDABAWA, kamar dai yadda za ku karanta kamar haka.

  • Rashin Jari Ke Hana Mawakan Kannywood Daukar Nauyin Mawaka Masu Tasowa -Nazifi Asnanic
  • Soyayya Ce Ta Yi Sanadin Fara Wakata – Princess Dabo

Da farko masu karatu za su so sanin sunanka.

Assalamu Alaikum warahmatullah. Sunana Sham’un Muhammad, wadda aka fi sani da Wizzamany Papers Neman Kudi Ambassador, daga Jihar Taraba Jalingo

Muna son ka ba mu tarihinka a takaice.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

Masha Allah, Ni an haifeni a Unguwar Malam Joda dake Garin Jalingo, na yi firamare a Central Primary School Jalingo, sannan na yi sikandirena sannan na yi sikandirena a Makarantar gwamnatin jeka-ka-dawo wato (Gobernment Day Hassan Secondary School Jalingo). Yanzu na ci gaba da Diploma a makarantar koyon Fasaha ta (Taraba State Polytechnic).

Me ya ja hankalinka ka fara waka.

To Alhamdulillah, abin da ya ja hankalina na fara waka ba komai bane illa na kasance mai son kallon fina-finan Hausa don hasali ma ni fim na ke so ba waka ba, amma Allah da ikonsa sai gashi na tsinci kaina a cikin masana’antar waka tsundum.

Me ya sa zabi waka, kuma a wane matsayi ka dauki waka?

Eh gaskiya na zabi na yi waka ce sakamakon ita ce hanya mafi sauki da za ka isar da duk wani sako da kake so suma gaskiya ina yin waka ne saboda jin dadi ba wai na dauke ta a matsayin itace na ke cin abinci da ita ba.

Wane irin nau’in waka kake yi, na soyayya ko kuma wacce ce?

To gaskiya ni mutum ne mai son yin soyayyah sosai, wannan ne ya sa na ga kamar ta inda zan fi aika sako na dawuri kenan. kuma kowacce ma na kan iya tabawa daga ciki ya danganta da abin da ya zo min a tunanina, amma gaskiya na fi yin wakar soyayya da kuma abin da ya shafi rayuwar yau da gobe. Sannan Alhamdu lillahi, ba shakka ni fashion designer ne gaba daya maza da mata, sannan ni dan baiwa ne domin ana dan Crypto.

Wane irin ci gaba ka samu a harkar waka?

To Alhamdulillah ci gaba gaskiya kullum karuwa yake yi saboda ci gaba na farko da na fara samu a rayuwata shi ne Arewa24 sun kira ni mun yi hira wadda wasu da kudinsu ma sun bukaci hakan ba su samu ba .

A bangaren abin hawa me ka taba mallaka

Alhamdulillah gaskiya ni yanzu babur nake da shi haijoue plus sannan na yi wata wakar jinjina an bani 100k for

Wace shekara ka fara waka?

Toh gaskiya na jima da fara waka amma ba na yin ta akai-akai ne saboda rashin jari ka san ita waka kasuwanci ne, to dai na fara waka tun 2015 ne gaskiya, amma wani lokaci na kan je hutu sannan na sake dawowa.

Wane kalubale la fuskanta a harkar waka ?

Eh gaskiya ina samun kalubale da wasu daga cikin dangi saboda gani suke ita waka shirme ce, sannan da kuma inda nake zama, ina waje ne inda duk zagewarka don ka burge su wallahi ba za su yaba ba amma Alhamdulillah a wasu wurare an karbe ni hannu bi biyu

Ka taba yin hira da wata kafar yada labarai a kasar nan a waje?

Eh na taba hira da Arewa 24 tb kamar yadda na fada maka a baya, sannan na yi hira da Liberty Radio Kaduna, sannan na yi hira da Bision FM Kano, sannan na yi hira da shimmo FM jalingo, kamar abokaina kuma akwai Fahada Danburam, KB.

Ina da ina a Nijeriya ko a kasar waje?

Aalhamdulillah gaskiya na je garuruwa da dama kamar su Abuja, Kaduna, Kano, Jos, kyauta da aka taba min kuma ita ne akwai wata waka da na taba yi mai suna turmi sha daka gaskiya an min kyautar da na ji dadi sosai

Menene burinka a rayuwa?

Eh to, gaskiya ni burina bai wuce a ce na samu recognition a duk inda na je ba, sannan na kasance mai tallafa wa sabbin kananun mawaka masu tasowa

Nawa ne yawan wakokinka, sannan da wace waka ka fara?

Gaskiya wakokin da na yi ba su da yawa wakata ta farko da na fara yi ita ce (daga Jalane)

Waye ya koya maka waka, wato ubangidanka?

Toh Alhamdulillah gaskiya ni ba ni da ubangida ko kuma wadda ya koya min waka, sai dai in ce abokan aiki na wato Elnur, Kaita, Starkid, Lilpee da dai sauransu.

Wace waka ka fi a cikin wakokinka?

Gaskiya duk wakar da na yi ina sonta sakamakon duk wakar da na yi tana yi min dadi, amma mutane sun fi son DAGA JALANE.

Ka taba yin kundin waka (Album) na bidiyo ko odiyo?

Eh ina da official bideos kuda 2 sannan ina da ep album guda 1 mai suna ya zan yi wanda yanzu haka yana nan akan all digital platforms idan aka yi searching na wizzamany papers duka za a gani.

A karshe wace shawara za ka ba wa matasa irin ka masu sha’awara yin waka?

Shawarata gare su itace abu na farko su yi karatu, sannan su nemi kudi kafin su fara harkar waka, saboda ita waka sei kana da jari idan ba ka da ba za ka taba jin dadin harkar ba kuma lamarin ba zai ta fi yadda kake so ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

October 25, 2025
Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 
Nishadi

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

October 11, 2025
Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?
Nishadi

Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?

October 11, 2025
Next Post
Nazari Kan Bunkasuwar Sin Bisa Yadda Aka Fitar Da Al’ummar Jino Daga Kangin Talauci

Nazari Kan Bunkasuwar Sin Bisa Yadda Aka Fitar Da Al’ummar Jino Daga Kangin Talauci

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

October 26, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

October 26, 2025
Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

October 26, 2025
Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.