Wa’adin da Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya dauka na yi wa kwamishinoninsa hisabi na auna kwazo ya cika, ana ganin wasu daga ciki za su amshi littafinsu da hannun hagu.
Idan za a iya tunawa dai lokacin da gwamnan Jihar Kano ya rantsar da kwamishinoni ya sanar da su cewa cikin watanni shida da rantsar da su zai waiwayi kokarin kowane kwamishina, wanda aikinsa ya gaza zaton da ake masa ko shakka babu gwamna ya yi alkawarin daga masa jan kati.
- Matakin Kona Kai Da Sojin Amurka Ya Dauka Ya Diga Ayar Tambaya Ga ‘Yan Siyasar Amurka
- Shirin Inganta Lafiya: An Duba Lafiyar Sama Da Mutum 2,213 A Zamfara
Yanzu haka kwimishinonin sun lakume wancan wa’adin, saboda haka kila kowane lokaci daga yanzu Gwamna Abba ya bukaci auna kokarin kwamishinonin.
Wasu daga cikin kwamishinonin sun yi ta gumi domin kar su amshi littafin hisabin gwazonsu da hannun hagu.
Gwamnatin Abba tana bin tsari jagoran darikar Kwankwasiyya na ba sani ba sabo, sannan kuma sabo da kaza baya hana yankata. Yanzu Jama’a sun zuba na mujiya domin ganin yadda sakamakon hisabin ayyukan kwamishinonin zai kasance, inda ko shakka babu wasu na shirin karbar littafinsu a hannu dama, ya yinda wasu kuma ke shirin karbar nasu a hannun hagu.
Akwai ma’aikatun da suke da alaka da talakawa kai tsaye, saboda haka ire-iren wadannan ma’aikatun talakawa ma na iya yi masu hisabi bisa abubuwan da suka bayyana, musamman yadda ake hangen wasu na kukan cewa gwamnatin ta makure komai an bar al’umma da kunci.
Sannan ana zargin a cikin kwimishinonin akwai ‘yan mowa da ‘yan bora, kasancewar wasu a ko da yaushe ludayinsu kan dawo yake.