• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wace Illa GB WhatsApp Ke Da Shi?

by Ibrahim Sabo
2 years ago
WhatsApp

Wace illa manhajar GB WhatsApp ke da shi? Wannan ita ce tambayar da ake ta yi min a kwanan nan, sakamakon yadda mutane suke ta sanarwa cewa, duk wanda yake amfani da GB Whatsapp ya yi gaggawar goge shi.

Mene Ne Illar GB WhatsApp?

Mutane da yawa suna amfani da GBWhatsapp ne, saboda yana da wasu tsarurruka da ‘Whatsapp’ na asali ba shi da su, kamar irin su adana (sabing) na hoto, bidiyo, ko kuma kwafin rubutu daga ‘status(es)’ na mutane kai tsaye, ko boye alamar karantawa ko karbar sako, ko don yana nuna alamar in mutum yana online, ko don tura ‘file’ mai nauyi, ko boye groups/chats, ko rubuta sunan ‘group’ da harafai sama da 35, yin status da harufai 250, a takaice. GBWhatsapp  yana da wasu ‘features’ da normal whatsapp ba shi da su.

Amma, yana da kyau mutum ya sani cewa duk wadannan tarko ne na masu kutse ko madatsa ‘hackers’. Sun tsara shi ne ta yadda zai ba ka sha’awa sosai, fiye da manhajar WhatsApp na asali (normal Whatsapp), tare da ba ka damar wasan buya da ma’abota amfani da normal Whatsapp, musamma ma mata. Ka tura sako, a karanta, amma ba za ka ga alamar an karanta ba, sannan a duba status dinka ba tare da ka ga wanda ya gani ba.

To dai maganar gaskiya, kai tsaye, GBWhatsapp, ‘mod’ ne, ma’ana ba asalin Whatsapp ba ne. Asali an kirkire shi da ‘code’ (tsari) irin an Whatsapp na gaskiya, ba tare da samun lasisi daga kamfanin ba. Ina shawartar masu amfani da GBWhatsapp, da masu sha’awar amfani da shi, da su kauracewa manhajar saboda wadannan dalilai; shi GBWhatsapp ba sahihi ba ne daga asalin kamfanin Whatsapp, ‘AledMods’ ne suka yi shi, ba su da lasisi, kuma sun karya ka’idar kirkirar da ba da lamunin amfani da sirrikan jama’a. Shi ya sa ba za ka samu manhajar a Google Playstore (apk) ko AppStore (iOS, na Apple) ba. Kai! Ka ma taba ganin wani adireshi na yanar gizo na GBWhatsapp? Amsa babu, saboda ba su da gaskiya.

LABARAI MASU NASABA

Jami’ar Bayero Ta Yi Rashin Fitaccen Masanin Ilimin Harshe, Farfesa Hafizu Miko Yakasai

Wayar Da Kai Kan Barazanar Intanet A Rayuwar Al’umma (CYBER AWARENESS)

Mai amfani da GBWhatsapp, ya sani cewa duk wasu bayanai da suke cikin wayarsa, wannan manhaja na iya tattarewa, babu wani sirrin cikin wayarka da ba za su iya lekawa ba, sayarwa, ko amfani da shi a duk lokacin da suka dama.

Idan aka turo ma wani sako mai dauke da ‘birus’ GBWhatsapp ba shi da wasu matakan kare ka daga cutarwarsu. Kai! Shi ma kansa ‘spyware’ ne. Duk abin da kake a GBWhatsapp, tsirara kake, shi ya sa, yawancin wadanda ake musu kutse (hacking) na Whatsapp, masu amfani da Whatsapp Mods ne, irin su GBWhatsapp, WhatsappPlus, Whatsapp Gold, Clones, FMWhatsapp, OGWhatsapp, YOWhatsapp da sauransu.

GBWhatsapp ba ya restore (dawo da bayanai) a wasu lokutan, kamar yadda na fada a sama, asali manhajar ta saba wa tsarin Google, kuma ana backup ne (yawanci) da Google account. Shi ya sa, da zarar ya yi ‘edpire’ (wani lokaci) za ka rasa duk bayananka, har ‘groups’ da kake ciki, sai ka nemi a maida ka. Ka lura, a duk lokacin da ka dauko shi daga yanar gizo, in dai wayarka tana ‘security patching’ (kula da tsaro), za ta gargadeka cewa, wannan app din zai iya cutar da kai, ko bayananka, ba ka taba lura ba ko? In ka taba lura da haka, don me za ka yarda?

Kai tsaye GBWhatsapp na mayaudara ne, in ba su cuceka yau ba, za su iya cutar da kai gobe. Kuma a kowane lokaci, Whatsapp na asali, za su iya dakatar da mai amfani da ‘mods’ daga amfani da dandalin na har abada.

Daga farkon watan nan dai zuwa yanzu, GB Whatsapp ya fara goge ‘formatting’ na wayoyin mutane. Sai ka bude wayarka, sai ka ga an goge komai dake cikinta. Idan kana amfani da shi, ka yi gaggawwar cire shi, tun kan hakan ta faru da kai.

Amfanin Hakuri A Tsakanin Magidanta (2)

Sanin muhimmancin hakuri ne naga ya dace na sake yin wani rubutun na biyu domin ba sai a tsakanin Magidanta ba ne ake bukatar hakuri, duk wanda yake a Unguwa ko Gari ya dace yayi hakuri,abin ya dogara ne ga babba da yaro, mace da namiji ba domin komai ba sai sanin kowa ne da rarrafe yaro ya kan tashi. Sai da matukar hakuri za a iya samun zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Don haka duk Unguwa ko Gari aka samu zaman lafiya to ko shakka babu akwai hakuri tsakanin duk al’ummar da suke zama a wurin, duk wuraren da ake samun matsaloli da suke rikidewa su zama yaki a cikin Unguwa ko Gari, don haka sai an kai zuciya nesa kafin a samu hakuri har a cimma yanayi na zaman lafiya.

Hakuri a ko ina ne ake abin ayi koyi da shi ne abu na karshe wanda idan ba ayi shi ba ana iya shiga halin da na sani wadda keya ce domin a baya take,shi yasa akwai bukatar su Magidanta duk lokacin da aka samu wata rashin jituwa ko ina ne abu mafi dacewa shi ne ayi kokari, ayi hakuri,a samu ayi sasanci domin yin hakan ne zai kasance abin aikhairi a ko ina ne.Akasin haka kuma ana iya shiga rashin kwanciyar hankali wanda idan ba shi babu zaman lafiya.Shi yasa Magidanta suna da jan aiki tsakaninsu na ci gaba da hakuri da juna da kuma koyi da kowa yayi haka, matsawar babu hakuri to zaman lafiya bai ga wurin zama ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jami’ar Bayero Ta Yi Rashin Fitaccen Masanin Ilimin Harshe, Farfesa Hafizu Miko Yakasai
Da ɗumi-ɗuminsa

Jami’ar Bayero Ta Yi Rashin Fitaccen Masanin Ilimin Harshe, Farfesa Hafizu Miko Yakasai

September 5, 2025
Wayar Da Kai Kan Barazanar Intanet A Rayuwar Al’umma (CYBER AWARENESS)
Kimiyya Da Fasahar Sadarwa

Wayar Da Kai Kan Barazanar Intanet A Rayuwar Al’umma (CYBER AWARENESS)

April 19, 2025
Kariya Daga Soyayyar ‘Online’ Da Shagalta A Intanet
Kimiyya Da Fasahar Sadarwa

Kariya Daga Soyayyar ‘Online’ Da Shagalta A Intanet

March 8, 2025
Next Post
Daliban Jami’ar Jos 6 Da Aka Sace Sun Shaki Iskar ‘Yanci

Daliban Jami'ar Jos 6 Da Aka Sace Sun Shaki Iskar 'Yanci

LABARAI MASU NASABA

gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
ASUU

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025
Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.