Tun daga watan Nuwamban bara, da nufin goyon bayan Falasdinawa, dakarun Houthi na Yemen sun rika kaddamar da hare hare kan jiragen ruwan dake da nasaba da kasar Isra’ila a Bahar Maliya.
A watan Janairun bana ne kuma Amurka da Birtaniya suka fara kaddamar da hare hare kai tsaye kan kayayyakin yakin dakarun na Houthi, lamarin da ya dada ruruta yanayin da ake ciki.
- Za A Kara Bunkasa Hadin Gwiwar Tsaro Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka
- Karairayin Amurka Ba Za Su Yi Tasiri Ba
Yayin da aka fuskanci cikas a tsarin zirga zirgar hajoji zuwa sassan duniya ta ruwa, sakamakon dalilan nan na tsaro, layin dogo da ya hade kasar Sin da sassan Turai ya zamo madadi da duniya ke karkata gare shi. A halin yanzu ana ta samun karuwar bukatar hidimar da layin dogon ke bayarwa tsakanin kasashen Turai, inda suke kara bayyana bukatar samun hidimomin da za su maye gurbin wanda ake samu daga sufurin teku.
Alkaluman baya bayan nan sun nuna cewa, cikin ‘yan shekarun nan, jimillar zirga zirgar jiragen kasa na dakon hajoji tsakanin Sin da Turai ya haura 85000, inda ya zuwa yanzu, sama da jiragen kasa 2600 suka yi zirga zirga ta layin dogon a shekarar nan ta 2024 kadai.
A matsayin babban ginshikin gina shawarar ziri daya da hanya daya mai inganci, layin dogon Sin zuwa Turai ya riga ya shiga kasashen Turai 25, da birane 219.
Ko shakka babu, ba za a iya raba gudanar tattalin arzikin duniya da tsarin sufurin jiragen kasa da cinikayyar hajoji tsakanin sassan kasa da kasa ba. Karkashin yanayin tsaro da ake ciki yanzu, alfanu da gudummawar da layin dogo na Sin zuwa Turai ke bayarwa ba zai misaltu ba. Kuma hakan na nuna yadda shawarar ziri daya da hanya daya ta dace da burin duniya na dunkulewar tattalin arzikin kasa da kasa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)