Hukumar shirya jarrabawar fita daka makarantun sakandare ta Afrika ta yamma (WASSCE) ta bayyana ranar fara jarrabawarta ta 2023 wacce za ta dauki tsawon makonni bakwai, daga 8 ga Mayu zuwa 23 ga Yuni.
Hukumar shirya jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ta sanar da hakan ne a wani taron manema labarai na share fagen fara jarrabawar a ranar Alhamis a Legas.
Shugaban ofishin na kasa, Patrick Areghan, a nasa jawabin ya bayyana cewa, jimillar dalibai 1,621,853 a fadin makarantun gwamnati da masu zaman kansu 20,851 ne suka yi rijistar jarrabawar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB ke kammala jarrabawar shekarar 2023 na shiga manyan makarantu.