Hukumar shirya jarabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka (WAEC) ta sanar da wani sabon shiri, wanda zai bai wa dalibai damar sake wasu darusa da suka fadi a WASSCE a tsakanin watannin Janairu da Fabrairun 2025.
Wannan ya nuna gagarumin sauyi daga tsohon tsarin Hukumar WAEC, inda masu zana jarrabawar da suka yi tuntuɓe a wani darasi ko darusa sai sun jira lokacin zagayowar jarrabawar dalibai masu zaman kansu.
Shugaban hulda da jama’a na WAEC, John Kapi, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa a shirin JoyNews’AM a Ghana a ranar Talata, 31 ga watan Disamba.
Ya bayyana, cewa sabon shirin mai suna WASSCE PC1 zai samar da hanya mai sauri ga dalibai don sake zana jarabawar da suka fadi.
Don haka, Daliban da ke bukatar sake zana jarrabawar WASSCE cikin gaggawa saboda tuntuɓe da suka yi a jarrabawar da ta gabata, sai su ziyarci shafin yanar gizo na WAEC domin samun cikakken bayani.