Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Asabar, shida ga watan Safar, shekarar 1444 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S. A. W.
Daidai da uku ga watan Satumba, shekarar 2022. Da fatan yau za a gafarce ni saboda matsala ta wutar lantarki ban iya kalato muku labari ko daya ba.
- ‘Yan Takarar Jihar Kano Sun Gamsu Da Taron KJPF
- Za A Yi Zaman Makokin Elizabeth Na Kwanaki 7 Da Binne Ta
A ‘yan kwanakin nan wutar sai ci gaba da tabarbarewa take yi. A yini da kyar a samu wutar minti talatin.
Talaka zai ci gaba da biyan kudin zama a duhu a zamanin mulkin masu gaskiya. Ga Hamid Ali ma ya ce damfarar talakan Nijeriya ake yi da ake cewa wai ana biyan kudin tallafin mai. Ga ‘ya’yan talaka da suke karatu a jami’a wata shida suna gida ba karatu.
LAHADI
Gwamnatin Tarayya ta nanata cewa no work no pay ga malaman jami’a da ke yajin aiki. Wata dai na bakwai ke nan da gwamnati ta dakatar da albashin malaman da ke yajin aikin. Malaman sun ce ba gudu ba ja da baya.
Yajin aiki ya ci gaba. Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da wani rumbun tattara bayanai da adana su, na dukkan wanda wata hukuma ta tsaro ta kama.
Hukumomin ‘yan sanda suna nan suna bincikar wani dan sanda, da ake zargin ya nemi ya yi lalata da wata budurwa mai shekara 17 da aka tsare ta a ofishin ‘yan sanda.
Gwamnatin Tarayya, ta kara wa ministoci da manyan sakatarori da sauransu, yawan kudin alawus na tafiye-tafiye.
Hukumomin soja, sun bullo da wata horarwa ta soja ta dole ta mako shida, ga yara da suka kammala makarantar ‘ya’yan sojoji da aka fi sani da Military School.
Kotu ta wanke tsohon gwamnan Jihar Filato Jonah Jang, daga zargin da ake masa na ya wawuri wata Naira Biliyan shida da kusan rabi.
A Jihar Zamfara masu fashin jama’a sun yi fashin liman da masallata masu yawan gaske a lokacin sallar Jumu’a.
A Jihar Katsina masu fashin jama’a, sun je rugar fulani, suka yi fashin fulani da dabbobinsu. Haka nan masu bin jama’a har gida su yi fashinsu sun addabi mutanen Funtuwa.
Kungiyar Makira Waya ta Jihar Kaduna, za ta gudanar da wani babban taronta a Lahadin nan a Kaduna, inda aka gayyaci malamanmu da mu dalibai, mu gabatar da makaloli. Tawa makalar ita ce Dangantakar Makira Waya Da Kafofin Watsa Labaru.
LITININ
Shugaban Hukumar Kwastam Hamid Ali, ya sake jaddada cewa duk wani batu da ake yi na cewa ana tallafi ga man fetur, damfara ce kawai ake yi, take karewa a kan tallaka.
Kungiyar SERAP mai rajin kare hakkin talaka, ta nemi shugaban kasa Buhari, ya janye sunayen mutanen da ya aike wa Majalisar Dattawa ta amince da su a matsayin kwamishinonin zabe, wadanda ‘yan jam’iyyar APC ne, domin ba za su yi adalci ba a zabukan shekara mai zuwa.
Shugaban ‘yan sandan Nijeriya, ya ba da tabbacin babu wata barazana da za ta hana gudanar da zabukan shekara mai zuwa.
A wata daya kacal, Nijeriya ta samu gibin kudi Naira Biliyan 524 da ‘yan kai.
‘Yan Boko Haram sun kutsa wani masallaci suka kashe limamin da ke limancin sallah da sauran masallata da ke bin limamin sallah a Jihar Barno.
Ambaliya tana neman raba Jihar Gwambe da sauran jihohi da take makwabtaka da su. Wadanda suka yi fashin wani shugaban gundumar raya kasa a Jihar Zamfara, sun masa kudi Naira Miliyan Ashirin.
Makarantar horar da kananan hafsoshin ‘yan sanda da ke Wudil, ta koka a game da yadda jaridar Sahara Reporters, ta tasa makarantar a gaba tana neman sai ta ga bayanta.
A Jihar Kaduna, an kama masu yi wa mutane cinne ga masu fashin jama’a a unguwa, su uku da aka fi sani da INFORMANTS a yankin karamar hukumar Igabi.
TALATA
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ba da umarnin dakatar da yunkurin da ake yi na karin kudin kiran waya.
Lai da Magashi, sun ce kwanan matsalar tabarbarewar tsaro a Nijeriya ya kare sai dai uwarta ta haifi wata.
Gwamnatin Tarayya, ta kwace wasu kaddarori goma sha hudu, da suke da nasaba da dakataccen dan sanda Abba Kyari, ta kuma tsara tuhume-tuhume kusan 24 da take masa.
Yau ministan ilimi da shugabannin jami’o’i da iyayen jami’o’i da hukumomin gudanarwa na jami’o’i, za su taru domin tattauna yajin aikin da malaman jami’a suke kan yi.
A dai Jihar Kaduna, mahukuntan jami’ar Jihar Kaduna, sun ba malaman jami’ar zuwa jiya, ko su koma aiki, ko malaman su gani a kwaryar cin su ko ta shan su.
Kamfanin mai na kasa NNPC, ya ce Allah kuwa da gaske ne a kullum ana shan man fetur lita miliyan sittin da takwas a kasar nan.
A ta daya bangaren kuma da alamu za a kuma aukawa matsalar man fetur saboda dillalan man na shirin daka barkono su yi yaji.
Ana ta yabon kwamishinan tsara birane da raya su na Jihar Legas Idris, saboda sauka da ya yi daga kan mukaminsa, saboda rushewar da wani bene da ake kan gina shi a Lekki ya yi da zuwa yanzun an ciro gawar mutum shida daga baraguzan ginin.
Mutanen yankin Kinkinau da na Unguwar Mu’azu da ke cikin garin Kaduna, sun yaba wa dan takaran majalisar dokoki ta Jihar Kaduna na jam’iyyar APGA na mazabar Tudun Wadar Kaduna, Aminu Soja Gida Gida, saboda kokarin da yake yi bangaren tsaro har ya kafa JTF ta Unguwar Mu’azu da Kinkinau.
Ya kuma koya wa yara da mata sana’o’i na dogaro da kai, da ci gaba da taimaka wa marasa galihu.
Sojoji sun kashe kwamandojin ISWAP da Boko Haram su biyar, da mayakansu fiye da dari biyu a Jihar Barno.