Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin kan harkokin Turai da Asiya Li Hui, zai kai ziyara kasashen Ukraine da Poland da Faransa da Jamus da kuma Rasha, daga ranar 15 ga wata, domin tuntubar dukkan bangarori game da samar da mafita a siyasance ga rikicin Ukraine.
Da yake bayar da sanarwar, kakakin ma’aikatar Wang Wenbin, ya ce tun bayan fara rikicin Ukraine, kasar Sin ta kasance mai daukar matsayin sanin ya kamata ba tare da goyon bayan wani bangare ba, haka kuma ta bayar da gudunmuwa wajen inganta tattaunawa da cimma yarjejeniyoyi domin tabbatar da zaman lafiya.
A cewarsa, ziyarar wani bangare ne na yunkurin Sin na kyautata hanyoyin tattaunawa domin neman zaman lafiya, yana mai cewa, wannan ya nuna cewa har kullum, kasar Sin na mayar da hankali ne ga tabbatar da zaman lafiya. (Fa’iza)