Ƙungiyar ‘yan Jaridu (NUJ), ta ƙasa reshen jihar Kebbi, ta taya zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiyar wakilan kafofin yaɗa labarai wato “Correspondent Chapel”, murna nasarar lashe zaɓe, tare da buƙatar su martaba dokoki ƙungiyar NUJ a jagorancinsu.
Cikin wata takardar da Sakataren NUJ reshen jihar kebbi, ismail Adebayo, ya fitar ƙungiyar ta yaba wa shugabannin da suka kammala wa’adinsu kan irin kokari da suka yi na kawo ci gaba ga gareta tare da alfahari da su.
- An Yi Hasashen “Ne Zha 2” Zai Zama Fim Na Kagaggun Hotuna Mafi Samun Kudi A Duniya
- Jami’ar Bayero Ta Shirya Bikin Yaye Ɗalibai Karo Na 39
Sabbin shugabannin wakilan reshen ƙungiyar na Kafafen Yaɗa Labaran da an zaɓesu ne ƙarƙashin saidon wakilin war ƙungiya ta jihar a yammacin ranar Talata, inda Kabiru Wurma, na Kamfanin Jaridar LEADERSHIP ya yi nasara zama shugaba, da Muhammad Lawal na Kamfanin Dillancin Labarun Nijeriya (NAN), a matsayin Mataimakin Shugaba,
Sauran waɗanda suka samu nasara sun haɗa da Olarenwaju Lawal, na jaridar Sun a matsayin sakatare, da Zubairu Tatu na Jarida Authority a Matsayin sakataren kuɗi, inda Binta Aliyu Abdullahi, ta samu mataimakiyar sakatare, da Umar faruk Abdullahi na LEADERSHIP HAUSA a Matsayin Mai binciken Kuɗi wato (Auditor), Aminu Umar na Jaridar Legacy, kuma ma’ajin kudi wato (Treasurer).
Bugu da ƙari NUJ a jihar ta buƙaci sabbin shugabannin da aka zaba su tabbatar da suna amfani da dokokin tsarin mulkin ƙungiyar yayin gudanar da ayyukansu na yau da kullum, kana daga ƙarshe uwar kungiya ta yi musu fatan alhairi na gudanar da kyakyawan jagorancin ga mambobinta