kungiyar ‘yan Jaridu (NUJ), ta kasa reshen Jihar Kebbi, ta taya zababun shugabannin kungiyar wakilan kafofin yada labarai murna nasarar lashe zabe tare da bukatar su martaba dokoki kungiyar NUJ a jagorancinsu.
Cikin wata takardar da Sakataren NUJ reshen Jihar Kebbi, Ismail Adebayo, ya fitar, kungiyar ta yaba wa shugabannin da suka kammala wa’adinsu kan irin kokari da suka yi na kawo ci gaba tare da alfahari da su.
- Wakilin Musamman Na Shugaba Xi Zai Halarci Taron Koli Kan Fasahar AI A Faransa
- Bayan Shekara 32 NPA Ta Samu Sahalewar Gwamnati Na Ƙara Haraji
Sabbin shugabannin wakilan reshen kungiyar na Kafafen Yada Labaran da aka zabe su ne karkashin sa idon wakilin kungiya ta jihar a yammacin ranar Talata, inda Kabiru Wurma, na Kamfanin Jaridar LEADERSHIP ya yi nasara zama shugaba, da Muhammad Lawal na Kamfanin Dillancin Labarun Nijeriya (NAN), a matsayin mataimakin shugaba,
Sauran wadanda suka samu nasara sun hada da Olarenwaju Lawal, na jaridar Sun a matsayin sakatare da Zubairu Tatu na Jarida Authority a Matsayin sakataren kudi, inda Binta Aliyu Abdullahi, ta samu mataimakiyar sakatare, da Umar faruk Abdullahi na LEADERSHIP HAUSA a matsayin mai binciken kudi da Aminu Umar na Jaridar Legacy, a matsayin ma’ajin kudi.
Bugu da kari, NUJ a jihar ta bukaci sabbin shugabannin da aka zaba su tabbatar da su na amfani da dokokin tsarin mulkin kungiyar yayin gudanar da ayyukansu na yau da kullum, kana daga karshe uwar kungiya ta yi musu fatan alhairi na gudanar da kyakyawan jagorancin ga mambobinta.