Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kiran da a aiwatar da matakan gaggauta dakatar da bude wuta tsakanin Falasdinu da Isara’ila, yana mai bayyana yanayin da sassan ke ciki a matsayin mai matukar bukatar shiga tsakani, don haka ya wajaba a shawo kan sa ba tare da bata lokaci ba.
Zhang Jun, ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a, ya kuma kara da cewa, sake barkewar fada tsakanin sassan biyu na nuni da cewa, ba za a iya shawo kan lamarin ta aiwatar da kwarya kwaryar matakai ba. Ya ce Sin na goyon bayan kungiyar kasashen Larabawa, da sauran kasashen Larabawa wajen taka rawar da ta dace kan lamarin.
A yau Asabar ne, an gudanar da taron wanzar da zaman lafiya a Gaza, a birnin Alkahiran kasar Masar. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp