Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Fu Cong, ya bayyana a gun taron kwamitin sulhu na MDD game da yankin manyan tabkuna na Afirka a ranar 16 ga wata cewa, sakamakon ci gaba da kai hare-hare na kungiyar M23 a baya-bayan nan, ya ta’azzara yakin gabashin Kongo DRC, kuma daukacin yankin manyan tabkuna sun fada cikin rudani. Dole ne kasashen duniya su yi aiki tare kuma su hada kai don kawar da wannan mummunar yanayin cikin gaggawa.
Fu Cong ya jaddada cewa, dole ne a gaggauta tsagaita bude wuta domin hana shi ci gaba da ruruwa. Babu wata hanyar soji da za ta magance rikicin gabashin Kongo DRC, kuma tattaunawa ta siyasa ita ce kawai mafita. Dole ne kasashen duniya su dauki kwararan matakai don tallafa wa kasashen yankin manyan tabkuna wajen magance tushen matsalolin da ke haifar da gazawar shugabanci da rashin daidaituwar ci gaba a yankin. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp