Kafofin watsa labaru da dama na kasar Japan, sun bayar da labarai a kwanakin baya, wadanda ke cewa a gun taron kolin kungiyar G7 da za a gudanar a Japan, za a bukaci kasar Sin ta bi ka’idojin kasa da kasa.
To sai dai kuma hakan ya baiwa sassan kasa da kasa mamaki, inda ake tambayar shin wadanne irin ka’idoji ne na kasa da kasa ake nufi?
A matsayin su na wadanda suka sha sabawa ka’idojin kasa da kasa, kasashen yammacin duniya, kamar su Amurka, ba su cancanci zargin kasar Sin a wannan bangare.
Game da ka’idojin kasa da kasa, wato ka’idojin raya dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, bisa tushen kundin tsarin mulkin MDD da ka’idojin majalissar, kasashen yammacin duniya da kasar Amurka ke wakilta, ba su ambato kundin tsarin mulkin MDD ba. Maimakon hakan sun fi mayar da hankali ga “ka’idojin kasa da kasa”.
A baya can wani wakilin Sin ya taba tambaya a gun taron kwamitin sulhun MDD cewa, wadanne irin ka’idoji ne na kasa da kasa da su kan ambata cikin maganar su? Kuma wane ne ya tsara irin wadannan ka’idoji? Kuma ko akwai wata alaka tsakanin ka’idojin su da hakikanin ka’idojin kasa da kasa?. Har yanzu dai, kasashen yammacin duniyar ba su amsa wadannan tambayoyi ba.
Manazarta dai na ganin wadannan ka’idoji ne kawai da suke furtawa, domin boye manufar kungiyar G7, ta aiwatar da matakan tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe, da tada tarzoma, da adawa da juna a tsakanin kungiyoyi daban daban. Irin wadannan ka’idoji sun samar da moriya ga wasu kasashe kamar Amurka, amma ba ga dukkanin kasashen duniya ba.
Ya kamata sassan kasa da kasa su tattauna game da harkokin duniya tare, domin kuwa wasu kasashen yammacin duniya ba za su iya wakiltar dukkan kasashen duniya ba.
Kuma wani abun tambayar shi ne wane ne ke sabawa ka’idojin kasa da kasa? Ya kamata kasashe membobin kungiyar G7 su amsa da kansu. (Zainab)