Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya bayyana a jiya cewa, manufar kasar Sin daya tak a duniya, ita ce ta tabbatar da zaman lafiya a mashigin tekun Taiwan.
Wang ya bayyana hakan ne a lokacin da aka tambaye shi, kan musabbabin tashin hankalin da ake fama da shi a mashigin tekun Taiwan da kuma yadda za a wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun na Taiwan, yayin da ya gabatar da jawabi game da manufofin kasar Sin game da nacewa kan bude yankin tare da amsa wasu tambayoyi a sakatariyar kungiyar kasashen ASEAN.
Da yake jaddada cewa, batun yankin Taiwan shi ne ginshikin babbar moriyar kasar Sin.
Wang Yi ya bayyana cewa, kiyaye ikon mulkin kasa da cikakkun yankuna, wani nauyi ne da ya rataya a wuyan duk wani Basine, kuma babu wani mutum, ko karfi ko wata kasa da za ta yi mafarkin raba yankin Taiwan da kasar Sin.
Wang ya ce, a baya-bayan nan, kasar Amurka ta sha jaddada cewa, za ta kiyaye ‘yancin kai da kuma yankunan kowace kasa, kuma kasar Sin tana mai da hankali sosai, kan yadda take martaba ka’idojin dangantakar kasa da kasa da manufofin MDD.
Amma Wang Yi ya bayyana cewa, bisa la’akari da tarihin Amurka, a gefe guda, dole ne a jaddada cewa, bai kamata Amurka ta rika nuna fuska biyu, da yin kwangaba-kwan baya, da kuma sauya matsayinta ba.
A jawabin nasa, Wang ya ce, yankin Asiya yana cikin wani sabon matsayi na tarihi, yana kuma fuskantar damar samun ci gaba da ba a taba ganin irinsa ba. Kasar Sin ta zabi yin hadin gwiwa da mambobin kungiyar ASEAN da sauran kasashen yankin, don tsayawa tsayin daka kan manufar samun zaman lafiya, da ci gaba, da ‘yancin kai da kuma damawa da kowa.
Wang Yi ya ce, kamata ya yi kasashen Sin da Amurka, su kulla kyakkyawar mu’amala a yankin Asiya da tekun Pasifik. Yayin da aka tambaye shi game da yunkurin da Amurka da sauran kasashe ke yi na karfafawa da fadada karfinsu a yankin kuwa.
Ya jaddada cewa, babu wani abin kirki da ya wuce kasashen Sin da Amurka su cimma kyakkyawar mu’amala a yankin, wanda ba wai kawai zai taimaka wajen kara kyakkyawar fata ga kasashen biyu ba, har ma zai gamsar da tsammanin da baki dayan kasashen yankin ke yi. (Ibrahim)