Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce Sin na maraba da dukkanin yunkuri na dawo da zaman lafiya da kare rayuka a Gaza, yana mai kira da a aiwatar da matakan wanzar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
Wang, ya yi tsokacin ne yayin da yake gabatar da matsayar kasar Sin dangane da kashin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta, da musayar fursunoni da aka cimma tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas, a taron manema labarai tare da memban majalisar zartarwar Switzerland, kuma ministan wajen kasar Ignazio Cassis.
Wang, ya yi kira ga daukacin sassa masu ruwa da tsaki kan batun, da su rungumi matsayar kasa da kasa dangane da manufar nan ta Falasdinawa su mulki kan su, yana mai jaddada cewa, duk wani tsari na gaba da za a amincewa da shi game da Gaza, dole ya martaba cikakkun muradun al’ummun Falasdinu.
Ministan wajen na Sin, ya kuma jaddada muhimmancin goyon bayan manufar kafa kasashe biyu masu cin gashin kai. Ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da sassan kasa da kasa, ciki har da Switzerland, ta yadda za a kai ga cimma nasarar aiwatar da sahihan matakan wanzar da zaman lafiya da daidaito a Gabas ta Tsakiya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)