• English
  • Business News
Sunday, August 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wang Yi Ya Gana Da Baki Amurkawa Bi Da Bi

by CGTN Hausa
1 year ago
in Daga Birnin Sin
0
Wang Yi Ya Gana Da Baki Amurkawa Bi Da Bi
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da shugaban hukumar manyan shugabannin zartaswa na kwamitin kasar Amurka mai lura da dangantakar Amurka da Sin Evan Greenberg, da shugaban kwamitin Steve Orlins, da kuma farfesa Graham Allison na jami’ar Harvard bi da bi a birnin Bejing.

Yayin ganawarsa da Evan Greenberg, da Steve Orlins, Wang Yi ya jadadda cewa, matsalar dake tsakanin dangantakar Sin da Amurka ita ce bangaren Amurka ya dauki Sin a matsayin abokiyar takararta mafi girma, da kasancewa kalubalen siyasarta mafi girma, irin wannan fahimta ta kuskure ta haddasa matsaloli ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Ya ce kamata ya yi bangaren Amurka ya yi tafiya a kan hanya guda tare da Sin, ta yadda za a iya inganta dangantakar kasashen biyu wajen samun daidaito, da kyautatuwa da kuma ci gaba.

  • Sin Ta Yi Tir Da Harin Ta’addanci A Pakistan Tare Da Kira Da A Gudanar Da Cikakken Bincike
  • Masu Satar Mutane Za Mu Dauke Su A Matsayin ‘Yan Ta’adda – Tinubu

Bangaren Amurka ya bayyana cewa, ci gaba da mu’ammala da juna, da tabbatar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, zai haifar da ci gaba a kan hanya mai dacewa, zai kuma samar da alheri ga duk fadin duniya. Kaza lika kwamitin kasar Amurka na dangantakar Amurka da Sin, yana fatan a samu ci gaba, da ba da gudummawa ga mu’ammalar kasashen biyu.

Yayin ganawarsa da Graham Allison kuwa, Wang Yi ya ce ya kamata Sin da Amurka su tinkari kalubalolin kasa da kasa tare, ta yadda za a gina dangantaka cikin kwanciyar hankali da dorewa.

Allison ya bayyana cewa, dole ne Amurka da Sin su yi hadin gwiwa, dole ne su samu hanya mai dacewa ta kulla huldarsu. Har ila yau, ya yi fatan kara fahimtar manufar diplomassiyar Sin ta hanyar fahimtar tarihi, da al’adu masu zurfi na kasar. (Safiyah Ma)

Labarai Masu Nasaba

Philippines Za Ta Girbi Sakamakon Rura Wutar Rikici Kan Taiwan

Jakadan Kasar Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministar Kula Da Masana’antu Da Cinikayya Da Zuba Jari Ta Kasar

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Naira Za Ta Ci Gaba Da Farfadowa, in ji  Shettima

Next Post

Kasar Sin Na Farin Cikin Ganin An Gudanar Da Babban Zaben Kasar Senegal Cikin Kwanciyar Hankali Da Lumana

Related

Philippines Za Ta Girbi Sakamakon Rura Wutar Rikici Kan Taiwan
Daga Birnin Sin

Philippines Za Ta Girbi Sakamakon Rura Wutar Rikici Kan Taiwan

13 hours ago
Jakadan Kasar Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministar Kula Da Masana’antu Da Cinikayya Da Zuba Jari Ta Kasar
Daga Birnin Sin

Jakadan Kasar Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministar Kula Da Masana’antu Da Cinikayya Da Zuba Jari Ta Kasar

14 hours ago
Andrei Okounkov: Sinawa Na Daukar Koyon Abubuwa Da Muhimmanci 
Daga Birnin Sin

Andrei Okounkov: Sinawa Na Daukar Koyon Abubuwa Da Muhimmanci 

15 hours ago
Kayayyakin Sin Sun Samu Karbuwa Yayin Bikin Nune-nunen Kayayyakin Abinci Na Afrika
Daga Birnin Sin

Kayayyakin Sin Sun Samu Karbuwa Yayin Bikin Nune-nunen Kayayyakin Abinci Na Afrika

16 hours ago
Kasar Duniyar Wata Da Kasar Sin Ta Samo Ta Samar Da Sakamakon Nazari Fiye Da 150
Daga Birnin Sin

Kasar Duniyar Wata Da Kasar Sin Ta Samo Ta Samar Da Sakamakon Nazari Fiye Da 150

17 hours ago
Xi Jinping Ya Zanta Da Putin Ta Wayar Tarho
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Zanta Da Putin Ta Wayar Tarho

1 day ago
Next Post
Kasar Sin Na Farin Cikin Ganin An Gudanar Da Babban Zaben Kasar Senegal Cikin Kwanciyar Hankali Da Lumana

Kasar Sin Na Farin Cikin Ganin An Gudanar Da Babban Zaben Kasar Senegal Cikin Kwanciyar Hankali Da Lumana

LABARAI MASU NASABA

Jihar Kogi Ta Kafa Kotuna 9 Don Hukunta Masu Cin Zarafin Mata

Jihar Kogi Ta Kafa Kotuna 9 Don Hukunta Masu Cin Zarafin Mata

August 10, 2025
NDLEA Ta Cafke Masu Baburan Da Ke Kai Saƙon Muggan Ƙwayoyi A Abuja

NDLEA Ta Cafke Masu Baburan Da Ke Kai Saƙon Muggan Ƙwayoyi A Abuja

August 10, 2025
Shirin Iskar Gas Na CNG Abin A Yaba Wa Shugaba Tinubu Ne -Shugaban IPMAN Na Ƙasa

Shirin Iskar Gas Na CNG Abin A Yaba Wa Shugaba Tinubu Ne -Shugaban IPMAN Na Ƙasa

August 10, 2025
Nazari Kan Dalilin Da Ya Sa Kajin Gidan Gona Ke Samar Da Ƙananan Ƙwai 

Nazari Kan Dalilin Da Ya Sa Kajin Gidan Gona Ke Samar Da Ƙananan Ƙwai 

August 10, 2025
Abubuwan Da Suka Ja Hankalin Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Tsarin Noman Waken Soya

Abubuwan Da Suka Ja Hankalin Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Tsarin Noman Waken Soya

August 9, 2025
Philippines Za Ta Girbi Sakamakon Rura Wutar Rikici Kan Taiwan

Philippines Za Ta Girbi Sakamakon Rura Wutar Rikici Kan Taiwan

August 9, 2025
Cacar Baki Ta Ɓarke Tsakanin el-Rufai Da APC Kan Tazarcen Tinubu A 2027

Cacar Baki Ta Ɓarke Tsakanin el-Rufai Da APC Kan Tazarcen Tinubu A 2027

August 9, 2025
Jakadan Kasar Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministar Kula Da Masana’antu Da Cinikayya Da Zuba Jari Ta Kasar

Jakadan Kasar Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministar Kula Da Masana’antu Da Cinikayya Da Zuba Jari Ta Kasar

August 9, 2025
Sanatocin Da Ba Su Kawo Ƙudiri Ba Tun Bayan Ƙaddamar Da Majalisar Dattawa Ta 10

Sanatocin Da Ba Su Kawo Ƙudiri Ba Tun Bayan Ƙaddamar Da Majalisar Dattawa Ta 10

August 9, 2025
Andrei Okounkov: Sinawa Na Daukar Koyon Abubuwa Da Muhimmanci 

Andrei Okounkov: Sinawa Na Daukar Koyon Abubuwa Da Muhimmanci 

August 9, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.