Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Gabon Michael Moussa-Adamo, yayin da yake halartar babban taron MDD a birnin New York.
A yayin ganawar, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Gabon abokiya ce ta kasar Sin a nahiyar Afirka, kuma Sin tana son hada hannu da ita wajen raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, da taimaka mata wajen samun ci gaba da farfadowa cikin sauri don kawo karin moriya ga jama’ar kasar. Wang Yi ya bayyana cewa, Sin tana son tabbatar da adalci ba tare da la’akari da matsayin kasa ba, kana tana tsayawa tare da kasashe masu tasowa, ciki har da na Afirka, kuma za ta ci gaba da goyon bayan kasashen Afirka don samun ci gaba da farfadowa tare.
A nasa bangare, Moussa-Adamo, ya bayyana cewa, kasar Sin abokiya ce mafi girma ga kasar Gabon a fannonin tattalin arziki da cinikayya. Kuma Sin ta taimakawa kasar Gabon wajen kyautata ayyukan more rayuwa, da yaki da cutar COVID-19, kana kamfanonin Sin sun samar da muhimmiyar gudummawa wajen raya tattalin arzikin kasar, a don haka, gwamnatin kasar Gabon da jama’arta, ba za su manta ba. Ya kara da cewa, kasar Gabon abokiya ce ga kasar Sin, kuma za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, da kin amincewa da siyasantar da batun kare hakkin dan Adam.
Bugu da kari, yana son hada aikin farfado da kasar Gabon da na raya shawarar “ziri daya da hanya daya” don samun bunkasuwar tattalin arziki a fannoni daban daban. (Zainab)