Yau Alhamis, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da ministan kasar Faransa mai kula da harkokin Turai da sauran kasashen waje, Jean Noel Barrot a birnin Beijing.
Yayin ganawar, Wang Yi ya ce a lokacin da duniya take fama da yanayi mai cike da sauye-sauye da hargitsi, ya kamata kasashen biyu su nuna sanin ya kamata a matsayinsu na manyan kasashe tare da karfafa hadin gwiwa. Ya kara da cewa, kasar Sin na daukar Faransa a matsayin babbar abokiyar huldar cimma ci gaba mai inganci.
A nasa bangare, Jean Noel Barrot ya ce Faransa ta kuduri niyyar raya dangantaka mai karko da dorewa da kyakkyawar makoma da kasar Sin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp