Dan majalissar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar G20, da su nacewa aiwatar da matakan gudanar da cudanyar sassa daban daban a zahiri, domin wanzar da zaman lafiya, da ingiza ci gaban bai daya a duniya baki daya.
Wang, ya yi wannan tsokaci ne a ranar Juma’a, lokacin da yake halartar taron ministocin wajen kasashe mambobin G20 a Bali na kasar Indonesia.
Kungiyar G20 dandali ne na kasashe 19, masu samun saurin bunkasar tattalin arziki da tarayyar Turai EU. (Mai fassarawa: Saminu daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp