Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa, shekarar 2023 ta kasance shekarar nazari da samun nasarori a fannin diflomasiyyar kasar Sin, inda ya takaita muhimman batutuwa guda shida.
Wang ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a taron tattaunawa kan yanayin kasa da kasa da huldar kasashen waje na kasar Sin a shekarar 2023.
- Xi Ya Jaddada Bukatar Samun Cikakkiyar Nasara Wajen Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa
- Equatorial Guinea Za Ta Daukaka Huldarta Da Sin Zuwa Wani Sabon Matsayi, In Ji Shugaban Kasar
Ya kara da cewa, da farko, harkokin diflomasiyyar shugaban kasar Sin sun samu gagarumar nasara, baya ga wasu sabbin matakai da aka fito da su a harkokin diflomasiyya na babbar kasa mai sigar kasar Sin.
Na biyu, an samu ci gaba mai inganci wajen gina al’umma mai makomar daya ga daukacin bil’adama, tare da samar da wani sabon kuzari ga kokarin gina makoma mai haske ga bil’adama.
Na uku, an yi nasarar gudanar da taron dandalin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar ziri daya da hanya daya karo na uku, inda hadin gwiwa tsakanin kasashen dake raya shawarar ta kai wani sabon mataki mai inganci.
Na hudu, tsarin kungiyar BRICS ya samu karuwa mai cike da tarihi, matakin da ya kara sabon karfi ga hadin kai da hadin gwiwa a kasashe masu tasowa.
Na biyar, an gudanar da taron koli na Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya cikin nasara, wanda ya samar da wani sabon dandali na kyautata makwabtaka da hadin gwiwar abokantaka a yankin.
Na shida, kasar Sin ta taimaka wajen yin sulhu mai cike da tarihi a tsakanin kasashen Saudiyya da Iran, inda ta kafa wani sabon misali na daidaita batutuwan da suka shafi siyasa.
Wang ya kara da cewa, wadannan sun nuna siga, salo, da dabi’un Sinawa, kuma sun nuna yadda kasar Sin ke kara yin tasiri a harkokin kasa da kasa, da karfin ikon tafiyar da sabbin ayyuka, da kyakkyawar dabi’a a sabon zamani. (Mai fassara: Ibrahim)