A yau 6 ga wata ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya tattauna ta wayar tarho da Josep Borrell, babban wakili mai kula da harkokin waje da manufofin tsaro na kungiyar tarayyar Turai EU.
Borrell ya nuna jimaminsa game da bala’in ruwan sama da ambaliyar ruwa da aka yi a kasar Sin a baya-bayan nan, ya kuma jaddada cewa, bangaren Turai ya jajirce wajen raya kyakkyawar alakarsa da kasar Sin. Shi kuma Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin na ba da muhimmanci sosai ga ganawar tsakanin shugabannin kasar Sin da kasashen Turai da aka shirya gudanarwa cikin wannan shekara.
Bangarorin biyu sun kuma yi musayar ra’ayi kan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya kamar rikicin Ukraine da na Nijar. (Mai fassara: Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp