Yau Jumm’a 23 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken bisa bukatarsa.
Wang Yi ya yi nuni da cewa, wajibi ne bangaren Amurka ya mai da hankali kan halastattun muradun kasar Sin, tare da daina neman hana ci gaban kasar Sin da mayar da ita saniyar ware. Yana mai jaddada cewa, ya kamata bangarorin biyu su mayar da hankali wajen aiwatar da yarjejeniyar Bali da shugabannin kasashen biyu suka cimma zuwa manufofi masu dacewa da kuma ayyuka na zahiri.
A nasa bangare kuwa, Antony Blinken ya ce, Amurka na son tattaunawa da kasar Sin kan ka’idojin huldar dake tsakanin kasashen biyu, da gudanar da huldar da ke tsakanin Sin da Amurka bisa amana, da yin hadin gwiwa a fannonin da suka dace da moriyar sassan biyu.
Ya kara da cewa, bangaren Amurka na ci gaba da martaba manufar kasar Sin daya tilo a duniya, kuma ba ta goyon bayan ‘yancin kan Taiwan.
Bangarorin biyu sun kuma yi musayar ra’ayi kan Ukraine. Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan batun zaman lafiya, da manufofin yarjejeniyar MDD, da kokarin da kasashen duniya ke yi na samar da zaman lafiya.(Ibrahim)