Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya bayyana cewa, a shekarar 2022, kasar Sin ta fuskanci kalubale, kana ta ci gaba da aiwatar da manufofinta na diflomasiyya bisa kuduri mai kyau, yayin da ake nazari da bitar yanayin da duniya ke ciki gami da dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen ketare.
Wang ya bayyana hakan ne Lahadin nan a jawabin da ya gabatar a yayin taron tattaunawa kan yanayin kasa da kasa da alakar Sin da kasashen waje na kasar Sin.
Da yake bitar ayyukan diflomasiyya na kasar Sin a shekarar 2022 kuwa, Wang ya ce, harkokin diflomasiyyar shugaban kasar a kasashen duniya, sun samu gagarumar nasara tare da gagarumin biki daya bayan daya, kuma hakan ya sanya danba ga aikin diflomasiyyar kasar Sin baki daya.
Da yake karin haske game da gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing da ta nakasassu, Wang ya yaba da gasannin da aka shirya a matsayin “nasara masu ma’ana.”
Wang ya bayyana cewa, kafin da kuma bayan babban taron wakilan JKS karo na 20, shugaba Xi Jinping ya halarci tarukan koli na bangarori daban-daban guda 5, ya kuma gana da shugabannin kasashe fiye da 40, lamarin da ya haifar da kololuwar ganawar diflomasiyya guda uku da shugaban kasar ya yi a wannan shekara, da kuma fara aikin sabbin shugabannin JKS a harkokin kasashen waje na kasar Sin yadda ya kamata.
Wang ya kuma jaddada cewa, kasar Sin na ci gaba da yin watsi da nuna adawa da nuna talaka daga wani bangare da takarar maras dacewa, tare da tabbatar da kwanciyar hankali a dangantakarta da sauran manyan kasashen duniya.
Ya kara da cewa, kasar Sin tana adawa da kuskuren kasar Amurka game da manufofin kasar Sin, tana kuma nazarin hanyar da ta dace da kasashen biyu.
Wang ya yi kira ga bangaren Amurka da ya canza salonsa, da kara kyakkyawar fahimta game da kasar Sin, da bin kyawawan manufofin kasar Sin, da kuma yin aiki tare da kasar Sin wajen kafa ginshikai, masu tushe game da samun ci gaban zaman lafiya da kwanciyar hankali a dangantakar kasashen biyu wato Sin da Amurka.(Ibrahim)