Bisa rokon Amurka, Wang Yi, mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana darektan ofishin hukumar harkokin waje ta kwamitin kolin jam’iyyar ya yi kwarya kwaryar ganawa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, a yayin taron tsaro na Munich.
Wang Yi ya bayyana matsayin kasar Sin kan batun balan-balan dinta maras matuki da ya shiga samaniyar kasar Amurka bisa kuskure, inda ya nuna cewa, matakin da Amurka ta dauka wajen daidaita batun ya sabawa yarjejejiyar kasa da kasa da abin ya shafa. Kasar Sin ba ta amince da hakan ba, kuma ta nuna adawa ga Amurka.
Game da rikicin kasar Ukraine, Wang Yi ya ce, kasar Sin a ko yaushe tana taka rawar da ta dace ta hanyar martaba ka’idoji, neman kawo zaman lafiya, da sa kaimi ga yin shawarwari. A matsayinta na babbar kasa, ya kamata Amurka ta bayyana hanyar da za a bi wajen warware rikicin a siyasance, maimakon kara rura wutar rikici, ta kuma yi amfani da damar da ta samu wajen samun moriya. (Kande Gao)