Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a Juma’ar nan cewa, ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, zai ziyarci kasashen Namibia, da jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Chadi da Najeriya, tsakanin ranakun 5 zuwa 11 ga watan nan na Janairu, bisa gayyatar da gwamnatocin kasashen suka yi masa.
Ziyarar ta Wang Yi a wannan karo, za ta kasance karo na 35 a jere, da ministan harkokin wajen kasar Sin ke farawa da ziyartar kasashen Afirka a duk farkon sabuwar shekara, cikin ziyarce-ziyarcen kasashen waje. (Saminu Alhassan)














