Yau Alhamis, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta ce, daga ran 13 zuwa 18 ga wata ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi zai kai ziyarar aiki kasashen Masar da Tunisiya da Togo da Cote Di’voire bisa gayyatar da aka yi masa. Ministocin harkokin wajen Sin su kan mai da Afrika zangon farko a ziyararsu a sabuwar shekara a cikin shekaru 34 a jere. Bayan ya ziyarci Afirka, Wang zai ziyarci kasashen Brazil da Jamaica daga ranar 18 zuwa 22 ga watan Janairu bisa gayyatar da aka yi masa.
Ban da wannan kuma, Mao Ning ta ce, a matsayinta na kasa mai tasowa, kasar Sin tana da makoma iri daya da kasashe masu tasowa, tare da kiyaye moriyar kasashe masu tasowa. Hadin kai tsakanin kasar Sin da kasashe masu tasowa ba wai don samun nasara ko fuskantar kowa ba ne, illa dai kare zaman lafiya a duniya tare, da sa kaimi ga ci gaban duniya, da kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa.
Kazalika, game da zabe a yankin Taiwan kuwa, Mao Ning ta ce, kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma Taiwan wani yankinta ne da ba za a iya ware ba, Sin na matukar nuna adawa da duk wata mu’ammala a hukumance tsakanin Amurka da yankin. Dole ne, Amurka ta tsaya tsayin daka kan ka’idar kasar Sin daya tilo a duniya da hadaddun sanarwoyi guda 3 da kasashen biyu suka amincewa, kada ta tsoma baki a zabukan yankin ta kowace fuska don kaucewa haddasa babbar illa ga huldar kasashen biyu da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Taiwan. (Amina Xu)