Xi Jinping, shugaban kasar Sin, kana babban sakataren jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ya halarci bikin kaddamar da sabon zangon karatu na kwalejin kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, jiya Laraba, inda ya yi jawabin cewa, kwalejin mai tarihin tsawon shekaru 90 yana da daraja ta musamman.
Shugaban ya yi tsokaci kan aikin kwalejojin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), inda ya ce, ya kamata kwalejojin su horar da jami’ai bisa bukatar jam’iyyar, kana su ba da shawarwari bisa yunkurin JKS na daidaita wasu matsalolin da ake fuskanta. A cewar shugaban, kwalejin jam’iyyar na da muhimmanci sosai a fannin horar da jami’ai, saboda haka kamata ya yi kwalejojin JKS su kara taka muhimmiyar rawa a kokarin horar da jami’ai masu kwarewa, wadanda za su iya sauke nauyin dake bisa wuyansu na farfado da al’ummar kasar Sin.
Shugaban ya kara da cewa, ya kamata kwalejojin JKS na matakai daban daban su kara kokarin gadon tunani irin na Karl Max, da koya ma dalibai dabarun gudanar da gyare-gyare, da raya kasa, da tabbatar da kwanciyar hankali, da amsa musu tambayoyin da suka samu, don samar da karin gudummowa ga kokarin gina kasar zamani mai bin tsarin siyasa na gurguzu, da daukaka matsayin al’ummar Sinawa a idanun mutanen duniya. (Bello Wang)