Shugaban ƙasar Somalia Hassan Sheikh Mohamud ya tabbatar da cewa aƙalla mutum 100 ne aka kashe sakamakon wasu hare-haren ƙunar baƙin wake biyu da aka kai da motoci a wajen ma’aikatar ilimi ta ƙasar.
BBC ta rawaito cewa; An kai harin ne a jiya Asabar a Mogadishu babban birnin ƙasar. Shugaban ƙasar ya bayyana cewa akwai aƙalla mutum 300 da suka samu raunuka sakamakon wannan harin.
- Sojojin Somaliya Sun Kashe Mayakan Al-Shabab Sama Da 100
- An Yaba Da Ra’ayin Kasar Sin Kan Zaman Lafiya Da Ci Gaba A Yankin Kahon Afirka
Mista Mahmud ya kai ziyara wurin da aka kai harin inda waɗanda suka shaida lamarin suka bayyana cewa cikin mintoci kaɗan motocin suka ƙaddamar da hare-haren.
Shaidu sun bayyana cewa ita motar ta biyun ma ta kai harin ne a yayin da jama’a suka garzayo da kuma motar ɗaukar marasa lafiya domin kai agaji.
Babu wata ƙunigiya da ta ɗauki nauyin kai harin zuwa yanzu amma ƙungiyar al-Shabab da ke da alaƙa da Al-Qaeda ta sha ƙaddamar da irin waɗannan hare-hare.
Ƙungiyar ta al-Shabab ta yi sanadin mutuwar dubban mutane a ƙasar ta Somalia da kuma rabba miliyoyi da muhallansu.
A ƴan kwanakin nan gwamnatin ƙasar ta rinƙa zafafa hare-hare kan ƴan ƙungiyar, lamarin da ya jawo ita ma ƙungiyar ke zafafa hare-hare.
Ko a kwanakin baya sai da ƙungiyar ta kai hari a wani otel inda ta kashe mutane da dama.