Sabon injin jirage masu saukar Ungulu kirar kasar Sin samfuin AES100, ya samu shaidar amincewar inganci da damar sayar da shi a kasuwanni, matakin da ya kafa harsashin bunkasa samar da kayayyakin bukata a fannin kirar ababen hawa masu tashi kurkusa da kasa.
Kungiyar makera injuna ta kasar Sin ce ta sanar da wannan ci gaba a yau Alhamis, inda ta ce sabon samfurin injin shi ne irinsa na farko da aka kera a Sin bisa fasahohin kasar na kashin kai, wanda ke da fasahar karfin “kilowatt 1,000”, ya kuma yi nasarar cika darajar karko ta kasa da kasa. (Saminu Alhassan)