Wani kamfanin kasar Sin mai suna CGC, ya kammala aikin shimfida hanyar mota mai lamba 2 a kasar Comoros a shekaranjiya 5 ga wata, inda shugaban kasar Comoros, Azali Assoumani, da jakadan kasar Sin dake Comoros, Guo Zhijun, suka halarci bikin kammala aikin.
A gun bikin, shugaba Azali ya gode wa gwamnatin kasar Sin gami da kamfanin CGC wanda ya dauki nauyin gudanar da aikin, tare da yabawa sosai da ingancin aikin.
Tsawon hanyar mota mai lamba 2 ya kai kilomita 38, wadda ta zama daya daga cikin muhimman hanyoyin dake kudancin babban tsibirin Comoros. Kammala aikin shimfida hanyar, zai saukaka matsalar cunkoson ababen hawa dake addabar wurin, kuma an yi hasashen cewa, tsawon lokacin zirga-zirgar motoci zai ragu daga awa 3 zuwa minti 40. Kaza lika, lamarin zai taimaka ga habakar tattalin arzikin garuruwan dake kewayen hanyar, da kyautata zaman rayuwar mazauna wurin. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp