Wani mutum da ake zargin yana da taɓin hankali mai suna Denis ya kashe mutum ɗaya tare da raunata wasu uku a kauyen Buzzah da ke karamar hukumar Zing a jihar Taraba.
Lamarin da ya jefa mutane da yawa cikin fargaba, ya faru ne a karshen mako.
- ‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta
- Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC
Mutanen uku da suka samu munanan raunuka suna samun kulawar Malaman jinya a babban asibitin Zing.
An ce wanda ake zargi da kisan, sananne ne a garin Zing saboda yawo a kan tituna, sanye da fararen kaya yana yin kamar yana wa’azi.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, lamarin da ya faru da misalin karfe 11 na daren ranar Asabar, ya jefa al’ummar garin Zing da kewaye cikin rudani kan hakikanin yanayin lafiyar wanda ake zargin.
“Daga cikin wadanda suka jikkata akwai ’yan banga guda biyu, wadanda a baya suka yi kokarin hana wanda ake zargin shiga jama’a saboda irin halayyarsa,” in ji wani ganau.