Wani mutum ya kashe kan sa ta hanyar rataya a Unguwar Rumde-Baru, da ke karamar hukumar Yola ta Arewa a Jihar Adamawa.
Wata majiya mai tushe ta ce “mutumin zai kai shekara 29 zuwa 30, ya rataye kan sa ne sakamakon matsin halin rayuwar da yake ciki.
Haka kuma wani mazaunin Unguwar Ali Ibrahim, ya bayyana cewar “mutumin nan ya jima yana cewa wata rana zai kashe kansa saboda matsin halin rayuwa, muna ganin wasa yake sai ga shi yau ta tabbata.
“Idan ka gaza samar wa iyalinka abin da za su ci, idan ka gaza biya wa yaranka kudin makaranta, ka gaza biyan kudin wuta, me zai hana ka, ka nemi aikata abin da wannan mutum ya aikata?” ya tambaya.
“‘Yan Nijeriya na cikin wani mayuwacin hali, mutum ya wayi gari bai san me zai yi ya samu kwabo ba, ko ni da nake maka magana, ban san me iyalina za su ci nan gaba ba, muna rayuwa ne babu fata sam, idan da akwai fata haka ba zai faru ba.
“Ina fata gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu, za ta dauki matakin gaggawa kan matsanancin halin da ‘yan Nijeriya ke ciki,” in ji Ali Ibrahim.
Ita ma dai rundunar ‘yansandan jihar ta bakin kakakinta, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce tana gudanar da bincike bisa dalilan da ya kai ga mutuwar mutumin.
Nguroje, ya ce “jami’an ‘yansanda da kwararrun likitoci suna gudanar da bincike kan dalilan da suka kai ga aukuwar mutuwarsa,” in ji SP Yahya.