Cibiyar lura da harkokin teku ta kasar Sin dake karkashin ma’aikatar kula da albarkatu ta kasar, ta fitar da wani rahoto dake kalubalantar halaccin Amurka na gudanar da ayyuka bisa dogaro da “’yancin zirga-zirgar jiragen ruwa”.
Rahoton wanda aka fitar jiya, ya bayyana batun “‘yancin zirga-zirga” na Amurka a matsayin wanda ke tattare da ka’idoji da dokokin da Amurkar ta tsara da kan ta, wadanda suka saba da dokokin kasa da kasa da yadda kasashe da dama ke tafiyar da harkokinsu.
Ya ce abun da Amurka ke kira da “‘yancin zirga-zirga”, ba ya bisa doron dokar kasa da kasa, kuma yana lalata fassarar dokar da ma aiwatar da ita. Ya kuma bayyana cewa, matakin misali ne na abun da Amurka ta saba yi na dogaro da karfin soja wajen matsawa sauran kasashe lamba.
Har ila yau, rahoton ya ce, matakin na Amurka muradu da dabarunta na siyasar duniya kadai yake karewa, yayin da take dogaro da karfin soja wajen haifar da tsaiko ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankuna da ma tsarin harkokin tekun na duniya. Bugu da kari, ya soki ayyukan Amurka yana cewa, sun saba doka, ba su kamata ba, kuma suna nuna fuskoki biyu. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp