Wani tsuntsu da masana kimiyya suka ce an halicce shi kamar jirgin yaki ya kafa sabon tarihi a matsayin tsuntsun da ya fi kowane tsuntsun yin tafiya mai dogon zango a duniya.
Tsuntsun mai doguwar jela ya tashi daga Alaska da ke Amurka, inda ya sauka a New Zealand, bayan shafe kwanaki 11 yana tafiya ba tare da yada zango ba, abin da ke nufin cewa ya yi tafiyar a kalla kilomita 12,000.
- ‘Yan Nijeriya Su Shirya Fuskantar Wahalar Rayuwa A 2023 – Sanata Yusuf
- Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Tsige Shugaban NIRSAL, Aliyu Abdulhameed Kan Zargin Almundahanar Kudade
Masana kimiyyar sun ce sun rika bin sawunsa ta hanyar wata na’urar bibiya ta zamani.
Sun kara da cewa tsuntsaye nau’ukan wanda ya nuna wannan bajinta a yanzu, ba sa bacci yayin da suke tafiya, hasalima su kan iya tsamurewa don rage girman jikinsu ta yadda za su yi doguwar tafiya ba tare da wata gajiya ba.
Dakta Jesse Conklin, na kungiyar Global Flyway Network ta masana kimiyya da ke bincike kan halittu masu kaura ya ce: ”Suna da wani irin karfi na rashin gajiya.
”Akwai abubuwa da yawa a tattare da su. An halicce su tamkar tsarin jiragen yaki. Suna da dogwayen fukafukai da ke taimaka musu yin abubuwa tamkar na jirgin sama.”
Tsuntsun wanda jinsin namiji ne da ake wa lakabi da 4BBRW da ake alakantawa da launin shudi da ja da kuma fararen zobuna da aka makala masa a kafafunsa, an kuma makala masa wani dan karamin tauraron dan’Adam mai nauyin giram biyar a kasan bayansa, don bai wa masana kimiyyar damar bibiyar halin da yake ciki.
Yana daya daga cikin hudun da za su bar cikin laka a Alaska, inda a can ne suke rayuwa suna tsintar tsutsa da tanar da suka kasance abincinsu tsawon wata biyu.
Dakta Conklin ya kara da cewa: ”Alamu sun nuna tsuntsayen sun san a inda suke a fadin duniya.
Ba za mu iya bayani sosai ba amma dai kamar suna da wata taswira.
”Suna shawagi ta saman tekun Pacific tsawon kwanaki a inda babu dandagaryar kasa. Daga nan sai su shiga New Caledonia da Papua New Guinea inda ake da tsibirai kadan.”