• English
  • Business News
Sunday, November 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wannan Takarda Ta Nuna Tushen Manufar Kasar Sin

by CGTN Hausa
2 years ago
Kasar Sin

Abokaina, a ganinku, me ya kamata a ce takardar farko da mahukuntan wata kasa su kan gabatar a duk shekara ta kunsa?

A kwanakin nan, kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwar kasar suka gabatar da Takarda Mai Lamba 1 ta bana, wadda ta shafi ayyuka masu alaka da aikin gona, da raya kauyuka, gami da manoma. Shekaru 21 a jere ke nan da shugabannin kasar Sin suka gabatar da takarda ta farko a shekara da ta shafi wannan jigo.

  • Kasar Sin Ta Fitar Da Ka’idojin Cinikayyar Hayakin Carbon
  • CMG Ya Shirya Shagali Gabanin Liyafar Bikin Bazara A Geneva

To, sai dai me ya sa ake daukar aikin gona, da kauyuka, da manoma da matukar muhimmanci a kasar Sin?

Saboda da sai da aikin gona mai inganci ne ake iya tabbatar da cewa al’ummar kasar Sin fiye da biliyan 1.4 suke iya samun isasshen abincin da suke bukata. Kana kauyuka a nasu bangare, ba su kai birane a fannin ci gaban tattalin arziki ba, don haka dole ne a ba su karin tallafi. Yayin da ingancin rayuwar manoma ke zama wani muhimmin bangare da zai tabbatar da samun daidaito tsakanin al’umma, inda dukkansu za a wadatar da su a kasar ta Sin.

Wato ana mai da hankali kan aikin gona, da kauyuka da manoma a kasar Sin ne domin neman tabbatar da ci gaban kasa mai dorewa kuma cikin daidaito, da samun ingantuwar rayuwar jama’a a kai a kai. Sa’an nan tushen wadannan manufofi shi ne tunanin shugabannin kasar Sin na “Mai da jama’a gaban kome. ”

LABARAI MASU NASABA

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Wannan tunani ya yi tasiri kan manufofin kasar Sin na cikin gida da na waje. Saboda haka gwamnatin kasar tana raya aikin gona, da harkoki masu alaka da kauyuka da manoma a cikin gida, gami da neman gina “al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya” a duniya, inda take kokarin haifar da ci gaba a sauran kasashe masu tasowa.

A kasar Sin, don ganin an tabbatar da samar da isashen abinci, ana ta kokarin fito da sabbin fasahohin aikin gona da za su tabbatar da samun girbi mai armashi a gonaki. Yayin da a jihar Morogoro ta kasar Tanzania, wasu kwararru Sinawa sun yi kokarin yada fasaha mai inganci ta shuka masara, cikin shekarun da suka gabata, inda har yawan masarar da ake girbi a can ya ninka sau 3.

Ban da haka, a lardin Zhejiang na kasar Sin da na taba ziyarta, na ga yadda kauyuka su ke raya sana’ar da ta dace da albarkatunsu. Misali a kan yi kiwon kifi a wuraren dake dab da tabkuna, da raya aikin yawon shakatawa a wurare masu duwatsu. Sa’an nan, a kasar Kongo Brazaville, ana yawan noman rogo, wanda yake lalacewa da wuri yayin da ake ajiyewa da jigilarsu. Saboda haka, bisa la’akari da yanayin da ake ciki wajen gudanar da aikin gona a Kongo Brazaville, da bukatar dake akwai, Sinawa sun samar da wasu injuna na sarrafa rogo, inda ake nika shi zuwa gari a kasar, matakin da ya taimaka wajen raya masana’antu, baya ga taimakawa manoma samun karin kudin shiga.

Haka zalika a wani kauye mai suna Ping Di Cun dake kudancin birnin Beijing na kasar Sin, na ga yadda gwamnatin wurin ta zuba kudade, tare da dasa itatuwa, da gina wuraren shakatawa, da sabbin ban dakuna, don inganta zaman rayuwar mazauna kauyen. Yayin da a Najeriya, wani kamfanin sadarwa na kasar Sin shi ma ya saukaka zaman rayuwar manoma, inda injiniyoyinsa suka yi amfani da itatuwa wajen kafa ginshikai masu dauke da na’urar samar da wutar lantarki ta hasken rana, da na’urorin sadarwa, ta yadda hakan ya taimaki mazauna kauyuka wajen magance matsalolin sadarwa, ban da wannan kuma, an ba su damar cajin wayoyin salularsu kyauta.

Bisa wadannan misalai muna iya ganin cewa, manufofin kasar Sin na cikin gida da na hulda da kasashen waje suna da tushe iri daya, wato tunani na mai da hakki da moriyar jama’a gaban kome. Wannan ma wani dalili ne da ya sa ake iya tabbatar da gaskiya, da kauna, da nuna sahihanci, gami da samar da hakikanin sakamako, yayin da ake gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar
Daga Birnin Sin

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik
Daga Birnin Sin

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Daga Birnin Sin

Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 2, 2025
Next Post
Yawan Mutanen Da Ake Jigila A Bikin Bazara Ya Bayyana Farfadowar Tattalin Arzikin Kasar Sin

Yawan Mutanen Da Ake Jigila A Bikin Bazara Ya Bayyana Farfadowar Tattalin Arzikin Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

November 2, 2025
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025
Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

November 2, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su

November 2, 2025
Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

November 2, 2025
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 2, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya

November 2, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.