A ranar Laraba ne, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ratta wa wasu dokoki hannu suka zama doka.
Daga cikin dokokin akwai dokar habaka bincike na tsaro ta shekara ta 2022, wanda majalisar kasa ta amince da shi, inda ya zama doka a yanzu haka.
- Hukumar Harkokin Waje Ta NPC Ta Fitar Da Sanarwa Kan Kudurin Amurka Game Da Shigar Balan Balan Din Sin Samaniyar Amurka
- Sin: Ya Zama Wajibi A Binciki Fashewar Bututun Nord StreamÂ
Wannan bayanin yana cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin majalisa, Babajide Omoworare ya fitar a ranar Laraba a Abuja.
Sauran dokokin da shugaban kasa ya rattaba wa hannu suka zama doka a yanzu sun hada da na dokar hukumar kula da ‘yan gudun Hijira da kuma Bakin haure ta kasa ta shekarar 2022, da dokar hukumar bunkasa harkokin shakatawa ta Nijeriya ta shekarar 2022 da kuma dokar asusun dakin karatu ta majalisar kasa wanda aka samar a 2022.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp