Bayan da kasar Sin ta kyautata matakan yaki da cutar COVID-19, an kara kawo sauki ga zirga-zirgar mutanen Sin da waje, lamarin da kasa da kasa suka yi maraba sosai. Alal misali, mataimakin firaministan kasar Thailand da sauran manyan shugabannin gwamnatin kasar, sun yi maraba da zuwan masu yawon shakatawa na kasar Sin, a filin jirgin saman kasa da kasa. Amma wasu kasashe sun kayyade shigar masu yawon shakatawa na kasar Sin, lamarin da ya kawo illa ga hadin gwiwar yaki da cutar COVID-19 na duniya.
Amurka da Japan da Koriya ta Kudu, kasashe ne da suka kayyade shigar masu yawon shakatawa na Sin. Japan da Koriya ta Kudu, kasashe ne dake makwabtaka da kasar Sin, wadanda suke da alaka sosai kan tattalin arziki da kasar Sin, don haka babu dalilin da zai sa su kayyade shigar masu yawon shakatawa na Sin. Amma a matsayin muhimman kasashe kawayen Amurka a nahiyar Asiya, sun dauki matakan kayyade shigar masu yawon shakatawa na Sin, kamar yadda Amurka ta yi.
Bisa binciken da hukumar kula da harkokin yaki da cutar COVID-19 ta Koriya ta Kudu ta yi, an ce, ba a gano mutanen Sin da suka kamu da cutar COVID-19 nau’in XBB.1.5 da aka fi gano irinta a Amurka ba. Ana iya ganin cewa, idan Japan da Koriya ta Kudu suna son hana yaduwar cutar, kamata ya yi su yi kokarin hana shigar da cutar nau’in XBB.1.5 da aka fi samunta a Amurka. Kayyade shigar masu yawon shakatawa na Sin da kasashen suka yi, aiki ne na nuna bambanci ga Sinawa, kana akwai yunkurin siyasa kan wannan batu. (Zainab)