Wasu kungiyoyin Zamfarawa magoya bayan dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin kauran Namoda da Birnin Magaji Honorabul Aminu Sani Jaji, sun gudanar da wani gagarumin taro, inda suka bayyana aniyar su ta yin kira ga dan majalisar da ya fito takarar Gwamnan jihar Zamfara a zaben dake tafe.
A wani taro da suka gudanar a jihar Kaduna, kungiyoyin wadanda suka hada da tsoffin kwamishinoni da ‘Yan majalisun jiha da kungiyoyin matasa sun kuma bayyana goyon bayan su kan tazarcen shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 mai zuwa.
- Sanata Shehu Buba Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Da Rigakafin Shanu A Bauchi
- Dangote Ya Ɗauki Nauyin Bikin Baje Kolin Gidajen Afrika Da Mahalarta Ƙasashe 21
Tun farko da yake jawabi, jagoran gamayyar kungiyoyin, Alhaji Abubakar Aliyu Tsafe (dan Masanin Tsafe) ya ce babban makasudin shirya taron shi ne jaddada goyon bayansu ga jam’iyyar APC a matakin tarayya tare da mika kokon barar su ga dan majalisar, ya fito takarar gwamnan jihar Zamfara.
Shima da yake gabatar da nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC magoya bayan Aminu Sani Jaji a Zamfara, Honorabul Lawalli Attahiru Dogon Kade, ya bayyana dan majalisar a matsayin Mutum jajirtacce mai hannun kyauta da taimakon jama’a, inda ya ce mutum irin Aminu Sani Jaji ake nema a matsayin Gwamnan Zamfara, domin shi kadai ne zai kai jihar ga tudun mun tsira.
Lokacin da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, Honorabul Aminu Sani Jaji, ya gode wa al’ummar Zamfara bisa nuna kauna da yarda da suka yi mishi, inda ya sha alwashin yi musu sakayya akan haka.
“Dukkanin abubuwan da muke yi muna yin su ne domin al’umma, kuma jama’ar nan ita taga dacewa ta da in tsaya mata takarar gwamna, babu shakka na amince zan amsa kiran da suka yi mini domin fitar da Jihar Zamfara daga mawuyacin halin da take ciki “ in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp