Wasu mutum biyu, Philip Osando (40) da Philip Emmanuel (35) sun mutu a cikin wata tankar man dizel shatale-talen Baban Gwari, da ke kan titin zuwa Katsina.
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ne ya bayyana haka, ya ce hukumar ta samu wani kiran gaggawa da misalin karfe 08:20 daga wani sufeto Abubakar Surajo wanda ya kai rahoton faruwar lamarin.
- Gwamnan Kano Ya Gabatar Da Kasafin Kudin 2024 Na Naira Biliyan 350
- Kotu Ta Daure Dillalin Tabar Wiwi Shekara 10 A Kano
Ya ce, “A lokacin da jami’anmu suka isa yankin da misalin 8:2, sun gano wasu mutane biyu, Philip Osando dan kimanin shekara 40 da kuma Philip Emernual dan kimanin shekaru 35 da haihuwa, wadanda suke harkokin kasuwancinsu kan titin Katsina.
“An ce wadanda abin ya shafa an musu alkawarin ba su kyautar man dizel amma kuma sai sun shiga cikin tankin dizal din don kwashe datti da dagelon da ke kasan tankin, shi ne suka shiga don cika sharadin da aka gindaya musu kafin su karbi man dizal din. Lokacin da direban babbar motar ya iso sai ya yi kokarin kiran daya daga cikinsu a waya sai bai ji an daga wayar ba.
“Can kuma da aka duba cikin takin sai aka same su a kwance cikin tankin dizal sun suma. Daga nan ne aka yi kokarin fito da su, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsu.”
Abdullahi ya kara da cewa an mika gawarwakin mutanen biyu ga Sufeto Abubakar Surajo na ofishin ‘Yansanda na karamar Hukumar Dala, yayin da ake ci gaba da bincike don gano musabbabin rasuwarsu.