Shugaban kwamitin tsangayu na jihar Kaduna, Imam Bukhari Maraban Jos ya maida martani ga masu cewa kada a nada tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i a matsayin minista.
Shehin Malamin ya yi wannan martani ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai a yau Litinin, 31 ga Yuli, 2023.
Imam Bukhari ya ce, “Mun wayi gari, mu ka ga wani rubutu da wani ya yi game da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
“Mu a matsayin mu, mu na martaba gidan Shehu, kuma mu na yarda da duk abin da ya zo mana daga gare shi, saboda matsayin sa a addini. Amma wannan ba zai hana wasu ko wani ba ya yi amfani da rigar gidan Shehu su cusa kan su cikin siyasa don cutar da wani saboda manufar su ta siyasa.”
Imam ya ci-gaba da cewa, “Alhamdu lillah kowa ya sani, wasu daga cikin su sun fito sun bayyana ra’ayoyin su kan dan takarar da su ke so a zaba, yanzu kuma Allah ya ba ma wadanda ba su yi daidai da ra’ayoyin su ba, don haka ba daidai bane yanzu wani ya fito ya ce wai kada a ba wa Malam Nasir El-Rurai mukamin minista, saboda wai El-Rufai bai da abin fada a jihar Kaduna. In ya ce haka bai taimaki addini ba, ko bai taimaki almajirci ba, wannan ra’ayi ne, in bai gani ba da yawa sun gani.
“maganar almajirai a jihar Kaduna, abubuwan da su ka faru a baya, an zauna da mai girma gwamna tare da Malam Albani, an wuce wannan wurin. Ba daidai ba ne a dawo da maganar baya, domin a cimma wata manufa ta siyasa.
“Alhamdu lillah. Bayan maganar almajirai ta kauce, alkhairai da yawa sun biyo baya, don har sai da aka gina makarantun tsangaya 25 a fadin jihar Kaduna, bayan maganar korar almajirai, a yanzu haka ana gina tsangayu 11 wanda kowanne zai lakume N7,000,000.”
Malam Nasiru El-Rufai dan adam ne wanda zai iya kuskure kuma mu na rokon Allah ya yafe masa kurakuran sa, amma ya yi aiki matuka a jihar Kaduna.