Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani manomi mai shekaru 60 mai suna Kayode Ajayi da ‘yarsa a unguwar Laluba da ke karamar hukumar Asa ta jihar Kwara.
LEADERSHIP ta rawaito cewa, Ajayi da ‘yarsa lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa gida daga gonarsu da ke kauyen Laduba a ranar Litinin din da ta gabata ‘yan bindigar suka yi musu kwanton bauna suka yia awon gaba da su, har yanzu ba amo-ba-labari.
- Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sun Koka Kan Kwararar ‘Yan Bindiga Zuwa Jihohinsu
- An Maka Sarkin Ilorin A Kotu Kan Hana Bikin Gargajiya A Kwara
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Okasanmi Ajayi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga LEADERSHIP a Ilorin a ranar Talata.
Sai dai ya ce an kubutar da diyar manomin daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su din.
Ajayi ya ce an tura jami’an hukumar da ke yaki da masu garkuwa da mutane zuwa garin Laduba don kubutar da manomi tare da damke wadanda suka aikata laifin.
Ya kara da cewa jami’an ‘yan sanda suna aiki tare da hadin gwiwar mafarauta da ’yan banga wajen ceto wanda abin ya shafa.