Gidauniyar raya yankunan karkara ta kasar Sin ko CFRD a takaice, wadda ke gudanar da ayyukan yaki da fatara, ta mika sabuwar ma’ajiyar ruwan sama da ta gina a makarantar firamare ta Obaay, dake wajen garin Dukem mai nisan kilomita 33 daga gabashin birnin birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha.
An gudanar da bikin mika ma’ajiyar ruwan ta karkashin kasa ne a ranar Jumma’a, wanda hakan ya cika adadin irin wadannan wurare na ajiyar ruwa da gidauniyar ta gina zuwa 40. Kaza lika, gidauniyar ta kammala aiki ne da hadin gwiwar kamfanin gine-gine na XCMG, da nufin magance kamfar ruwa da ta jima tana addabar yankunan karkarar kasar Habasha.
- Hukumar Ilimin Bai Daya Za Ta Gina Dakunan Karatun Zamani A Makarantun Nijeriya
- Gwamnatin Tarayya Ta Rabar Da Naira Biliyan 16.1 Ga Masana’antu 22 — Ministan Kudi
Jami’an karamar hukumar yankin sun jinjinawa gidauniyar CFRD, da abokan huldarta, bisa kwazonsu na samar da ruwa mai tsafta ga al’umma.
Da take mayar da martani, daraktar ofishin CFRD na kasar Habasha Yin Qian, ta ce tun daga shekarar 2017, gidauniyar CFRD da kamfanin XCMG, sun yi hadin gwiwa wajen samar da irin wadannan ma’ajiyar ruwa, aikin da ya amfani sama da mazauna yankunan karkara 12,000.
Ana dai tsara ma’ajiyar ruwan ta yadda za ta dore, tare da amfani da salon gine-ginen da ake iya sabuntawa da saukin gudanarwa. (Saminu Alhassan)