Allahu Akbar! Kyawun karshe. Wata Malamar Islamiyya ta rasu tana tsaka da karatun Al-Qur’ani a dakin taro a kasar Indonesiya.
An tabbatar da hakan ne a wani Bidiyo da Shafin @muslimDaily ya daura a Shafin sa na Twitter.
Bidiyon mai tsawon minti 1:29 ya nuna yadda ta fadi tana tsaka da karatun Suratul Baqarah. Tana gab da faduwa tayi tsallake zuwa aya mai ce “Wa ilahukum ilahun wahid, Ku sani Ubangijinku Daya ne”.
Kasar Indonesiya, itace kasar da ta fi yawan mabiya addinin musulunci a fadin duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp