• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wata Miyar Sai A Makwabta…

by CGTN Hausa and Sulaiman
7 months ago
Makwabta

Babban abin da ake so a shugabanci a kowane irin salo shi ne sanya muradun ’yan kasa gaba da komai, domin duk abin da gwamnati za ta yi ya zamo don raya ’yan kasa ne.

A bisa tsarin shugabanci na kasar Sin, gwamnatin dake jan ragamar kasa kan fitar da rahoton ayyukan da za ta fi bai wa fifiko a duk shekara-shekara inda ake matukar kula da me al’ummar kasa ke so musamman mabukata da masu karamin karfi da kuma abubuwan da suka shafi ci gaban tattalin arzikin kasa.

  • Rashin Haɗin Kai Na Barazana Ga Makomar Arewa – Sarkin Zazzau
  • Gwamna Buni Ya Naɗa Matasa 200 A Matsayin Hadimansa

Wani abu da ya birge ni game da kundin rahoton ayyukan gwamnatin kasar na shekarar 2025 shi ne sabbin tsare-tsaren da aka fitar domin tallafa wa harkokin da suka shafi rayuwar jama’a wanda ke nuna cewa tabbas gwamnatin kasar tana muhimmanta muradun jama’a gaba da komai.

Bari mu duba wasu daga cikinsu musamman ta fuskar mutanen da tabbas an san suna bukatar tallafi kamar tsofaffi da kananan yara da kuma marasa aikin yi da ke zaune a birane.

Kundin rahoton ayyukan gwamnatin na shekarar 2025 ya bayyana cewa domin kara kyautata jin dadin rayuwar tsofaffi a kasar, an kara yawan kudin tallafin kula da su da mazauna birane marasa aikin yi da yuan 20. Haka nan a shekarar ta 2025 gwamnati ta sha alwashin bayar da tallafin kula da kananan yara tare da kara mayar da hankali a kan ayyukan da suka shafi hidimta wa yara kanana.

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

Idan ka dauki bangaren tsofaffi da kananan yara, za ka iya cewa su ne mafi rauni a cikin al’umma. Tsofaffi sun gajiya don haka suna bukatar taimako, yara kanana kuma ba su kawo karfi ba, bisa haka dole suna bukatar madafa. A nan, sai mu ce gwamnatin Sin ta yi tunani mai kyau.

Kundin rahoton ya kuma bayyana cewa, a shekarar 2025 gwamnatin kasar za ta kara zage damtse wajen raya kauyukan dake rabe da birane da gyara gine-ginen da suka tsufa. Ga duk wanda yake shiga yankunan kauyuka da ke cikin birane (kamar unguwannin masu karamin karfi) ko wadanda suke rabe da su zai ga ba su da kyawun gani, domin kayayyakin alatu da kayatattun gine-gine da ababen more rayuwa da ake samarwa a cikin birane ba za su taba bari taurarin wadannan kauyuka su haska ba. Domin tabbatar da ci gaba da zamanintar da kasar Sin yadda ya kamata, dole ne a tafi tare da ire-iren wadannan kauyuka cikin ayyukan ci gaba da ake gudanarwa.

Har ila yau, rahoton ayyukan gwamnatin ya bayyana cewa, a bana, gwamnatin kasar ta kudiri aniyar kara yawan kudin tallafin muhimman ayyukan inshorar kiwon lafiya ga mazauna karkara da marasa aikin yi na birane, inda aka kara yawan kudin da yuan 30 ga kowane mutum. Ko tantama babu, tabbas wannan zai kara inganta kiwon lafiyar al’umma musamman marasa karfi.

Bugu da kari, tallafin kiwon lafiyar bai tsaya nan ba, akwai wani kaso na musamman da gwamnatin za ta ware na tallafin kudin kiwon lafiya ga daukacin al’umma a bangaren muhimman bukatunsu inda shi ma aka kara yawansa da yuan 5 ga kowane mahaluki da zai ci gajiya.

Baya ga batun tallafi na zuwa asibiti, gwamnatin ta kuma yi wata farar dabara da za ta kara inganta koshin lafiya ta hanyar sanya gina dandaloli da dakunan wasannin motsa jiki a kusa da gidajen al’umma a cikin kundin rahoton ayyukanta na 2025. Wannan dabara za ta kara inganta kiwon lafiyar al’umma saboda kowa ya san yadda motsa jiki ya zama wajibi ga duk wanda yake son samun koshin lafiya.

Kazalika, da yake zamani na ci gaba da sauyawa ta fuskar komai da komai, gwamnatin kasar Sin ta sha alwashin hanzarta komawa amfani da tsarin biyan kudade na zamani da aka inganta domin kara saukaka hada-hada da harkokin kudade.

Duka wadannan abubuwa an bullo da su ne domin cimma muradun jama’a da kara kula da bukatunsu. A gaskiya ina kwadayin ganin irin wannan tsari a kasashenmu na Afirka, saboda muhimmanta bukatun jama’a alhaki ne da ke rataye a wuyar gwamnati. Ya kamata shugabanninmu su sa himma da kwazo don su raba mu da tunanin “wata miyar sai a makwabta”, a duk lokacin da muka ga yadda ake kula da muradun al’umma a wasu kasashe, musamman kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika
Daga Birnin Sin

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025
Gaza
Daga Birnin Sin

Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar?

October 16, 2025
Next Post
Gwamnatin Zamfara Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Kasar Sin Wajen Inganta Noma, Sufuri Da Ma’adanai 

Gwamnatin Zamfara Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Kasar Sin Wajen Inganta Noma, Sufuri Da Ma’adanai 

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
NAWIA

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025
Gaza

Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar?

October 16, 2025
Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

October 16, 2025
Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

October 16, 2025
Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

October 16, 2025
Tinubu

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025
Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

October 16, 2025
Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.