Wata babbar kotu a jihar Kano ta umarci ‘yansanda da su fitar da sarki Aminu Ado Bayero daga ƙaramar fadar masarautar Kano da ke Nasarawa. Kotun ta kuma ba da umarnin wucin gadi na hana bayyan kansa a matsayin Sarkin Kano.
Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ce ta bayar da wadannan umarni a matsayin martani kan ƙarar da babban mai shari’a na jihar Kano da wasu mutane suka shigar kan Aminu Ado Bayero da wasu sarakuna huɗu da gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf ya rushe
- An Shawarci Sarki Aminu Ado Ya Fice Daga Kano
- ‘Yan Majalisar Tarayya Sun Goyi Bayan Gwamnatin Kano Kan Mayar da Sarki Sanusi II
Har wa yau, Kotun ta umarci ‘yansanda da su gaggauta fitarwa tare da kange fadar masarautar da ke unguwar Nasarawa.
Duk da umarnin kotun, Sarki Aminu Ado Bayero na ci gaba da zama a ƙaramar fadar Nasarawa tare da tsauraran matakan tsaro, yayin da Sarki Sanusi II ke gudanar da mulki daga babban fadar masarautar, lamarin da ya haifar da ruɗanin kan yadda sarakunan biyu ke gudana da sha’anin sarauta.