Kimanin yara 10 ne ‘yan tsakanin shekaru 3 zuwa 13 aka rahoto sun rasa rayukansu sakamakon bullar wata cuta mai shake numfashi a garin Kafanchan da ke karamar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna.
Babban Daraktan lafiya (CMD) na asibitin ‘Sir Patrick Ibrahim Yakowa’, Dakta Isaac Nathaniel ne ya tabbatar da bullar cutar a Kafanchan inda ya ce har yanzun ba a gano musabbabin cutar ba.
Shugaban Karamar Hukumar Jema’a ta Jihar Kaduna, Honarabul Yunana Markus Barde, ya yi kira ga mazauna garin da su tashi tsaye sukai rahoton duk wani yaro mai shekaru kasa da 13 da ke fama da matsalar shakewar numfashi, ciwon makogwaro ko kuma yoyon majina a hanci ga hukumomin kiwon lafiya mafi kusa.
Shugaban ya bukaci mazauna garin da su lura da irin wadannan alamomin domin dakile yaduwar cutar da wuri kafin ta yi kamari.
Haka kuma an shawarci ma’aikatan kiwon lafiya a matakin farko a fadin kananan hukumomi, cibiyoyin maganin gargajiya, malaman addini, da iyaye da su dauki matakin da ya dace, ganin cewa, wasu iyaye da ‘yan uwa suna boye wasu daga cikin masu fama da cutar.
Ya ja hankali cewa, masu wannan dabi’a, sam hakan bai dace ba, annoba ta kan zama illa ga duk al’umma baki daya idan ba a hada guiwa an yake ta ba.
Daktan ya kara da cewa, kwararru daga babban birnin tarayya Abuja da jihar Kaduna za su zo garin domin kawo dauki, ya bukaci al’ummar karamar hukumar Jema’a da su bayyana duk wanda aka ga yana dauke da irin alamomin cutar ga hukumar lafiya ta matakin farko, da cibiyoyin gargajiya da sauran hukumomin da abin ya shafa domin gaggauta daukar mataki.