Kimanin mambobin jam’iyyar dubu 10,000 ne suka fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC a jihar Osun saboda abin da suka bayyana na iron aiyukan raya kasa na gwamna, Adegboyega Oyetola, tun da ya zama gwamna a 2018.
Wanda ya jagoranci taron masu sauya shekar shi ne, Hon. Wale Ojo, shugaban jam’iyyar PDP na jihar da Hon. Albert Adeogun, mataimakin dan takarar PDP a zaben gwamna na 2018 da kuma tsohon dan majalisar wakilai; Ayodele Asalu (Asler), dan takarar majalisar wakilai a mazabar tarayya ta Ede da kuma Soji Ibikunle, dan jam’iyyar.
Wadanda suka sauya sheka, daka sassa daban-daban, da suka hada da kananan hukumomi da mazabu da ke jihar, an karbe su a filin shakatawa na Freedom Park, Osogbo, babban birnin jihar, a ranar Talata.
A lokacin da yake karbar wadanda suka sauya sheka, sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata Iyiola Omisore, ya yi maraba da wadanda suka sauya shekar.
Omisore, wanda ya bayyana sauyin shekar tasu a matsayin abunda ya dace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp