Kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO ta kaddamar da taron karawa juna sani a jiya Laraba a Switzerland mai taken “Hadin gwiwar Sin da Afirka: ra’ayin WTO”, wanda ya mai da hankali kan ci gaban da taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin kan Sin da Afirka wato FOCAC ya samu.
Sin ta sauke nauyin jagorancin wannan taro, wakilan mambobin WTO fiye da 10 ciki har da Chadi da Afirka ta kudu wadanda suke kan matsayin masu shiga tsakani daga bangaren Afirka, da kuma Amurka da dai sauransu, da kuma jami’an WTO da cibiyar kasashe masu tasowa da saurin bunkasuwa da dai sauran kungiyoyin kasa da kasa sun halarci taron.
- Tinubu Ba Ya Nuna Wa Kowane Yanki Bambanci — Minista
- Ba Zan Goyi Bayan Ƙudirin Ƙarin Haraji Ga Talakawa Ba – Sanata Ndume
Taron ya tattauna kan ci gaba da taron Beijing na FOCAC ya samu, da kuma koyi da dabarun da Sin ta yi amfani da su na cire kashi dari na harajin kayayyaki daga kasashe mafi karancin ci gaba, da ma tattauna kan boyayyen karfin Sin da Afirka na gaggauta kwaskwarimar da ake yiwa WTO da raya huldar samun bunkasuwar tattalin arziki tare.
Wakilin dindindin na kasar Sin dake WTO Li Chenggang ya nanata cewa, Sin za ta kara hadin gwiwarta da mambobin WTO, da ma nuna himma da kwazo wajen ciyar da kwaskwarimar da ake yi kan WTO gaba, da ma kara azama ga samun ci gaba da yakini a taron ministoci karo na 14 na WTO da za a gudanar a nahiyar Afirka a shekarar 2026.
Wakilin Chadi dake WTO ya ce, hadin kan Sin da Afirka a matsayin misali ga hadin kan kasashe masu tasowa, zai iya gina tsarin cinikayya tsakanin mabambantan bangarori a bangaren adalci da ba da cikakken haske da hangen nesa, hakan zai samar da damammaki masu kyau ga bunkasuwar duniya baki daya. (Amina Xu)